Buhari na shan suka da yabo kan June 12

Buhari

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Jam'iyyar PDP ta ce akwai baki-biyu a matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka

'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da matakin da Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya dauka na karrama marigayi Moshood Abiola.

Shugaba Buhari ya ce zai bai wa marigayin babbar lambar girmamawa ta GCFR a ranar bikin tuna wa da ranar zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ta bayyana.

Hakazalika ya ce daga bana ranar 12 ga watan Yunin ce za ta zama ranar demokradiyya a kasar kuma ranar hutu, maimakon ranar 29 ga watan Mayu.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce akwai baki-biyu a matakin da shugaban ya dauka, domin ya yi aiki da gwamantin da Abiola ya mutu a hannunta.

"Idan Buhari da gaske ya ke game da kare demokuradiya to kamata ya yi ya rinka girmama kundin tsarin mulkin Najeriya," a cewarsa.

BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukanmu na sada zumunta bayan wallafa labarin ciki har da shafinmu na Facebook.

Wasu 'yan kasar sun bayyana jin dadinsu ga daukar matakin, yayin da wadansu suke nuna cewa wannan ba ita ce matsalarsu ba.

Alhajiji Mohd Usatu Akuyam: "Aikin banza ke nan. Ai ba wannan ba ce matsalar talakan Najeriya, domin matsalar 'yan Najeriya ita ce sassaucin kayan masarufi, tsaron rayukan al'umma, da samar da aikinyi ga matasa da sauransu."

Shi ma Maikudi Shu Aibu Waya cewa ya yi: "Ai ni Buhari ba za ka burgeni ba, sai lokacin da ka sauya sunanka zuwa Aremu Buhari, sannan ka koma Ogun da zama idan ka kammala mulkin ka, tun da dama su kake wa aiki."

Har ila yau akwai wadanda suka jinjina wa shugaban kan matakin da ya dauka:

Yusif Heluwa Dandume: "Ma Sha Allah. Wannan mataki ko matsaya da Shugaba Buhari ya dauka ya yi daidai kuma wannan ya kara tabbatar da gaskiyarka da rikon amanarka."

Abubakar Kawu Girgir: "Ko shakka babu Najeriya ba za ta taba mantawa da Abiola ba, don wannan matakin karrama shi da Shugaba Buhari ya yi daidai."

Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a - ku ma za ku iya bayyana ra'ayoyinku a shafin namu na Facebook:

Asalin hoton, Facebook