Tsige Buhari zai iya jawo yaki a Najeriya – Dan Majalisa

Bayanan bidiyo,

'Tsige Buhari kamar yaki ne'

Wani dan majalisar dokoki a Najeriya Lawal Yahaya Gumau ya bayyana barazanar tsige Shugaba Buhari a matsayin wani abu da zai iya jawo yaki a zauren majalisar dokokin kasar.

Dan majalisar, wanda yake wakiltar mazabar Toro a jihar Bauchi, ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga wadansu 'yan majalisar da ke barazanar tsige Shugaba Buhari.

'Yan majalisar dokokin kasar dai sun yi barzanar daukar mataki idan Shugaba Buhari bai aiwatar da wadansu bukatu 12 ba.

Dan majalisar ya ce tsige shugaban ba zai yiwu ba, domin a cewarsa, "talakawa suna son shi kuma suna jin dadin manufofinsa."

Har ila yau dan majalisar ya musanta zargin cewa shugaban yana nuna wariya wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Hakazalika ya zargi Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kokarin mayar da matsalar da yake da ita da rundunar 'yan sanda kasar zuwa matsalar majalisar.

Jerin kudurorin da 'yan majalisa suka cimma a zaman:

Asalin hoton, TWITTER/THE SENATE

 • Kawo karshen kashe-kashe a Najeriya
 • A daina tsangwama da kuma muzguna wa wadansu 'yan majalisa
 • Gwamnati ta rika bin doka da oda
 • Shugaban kasa ya dauki mataki kan wadansu wadanda ya nada mukamai
 • Ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa da Allah
 • Ya daina sanya baki kan al'amurran da suka shafi majalisar
 • Majalisar dokokin kasar za ta fara tuntubar Majalisar Dinkin Duniya don ceto demokradiyyar Najeriya
 • Majalisar za ta tuntubi kungiyoyi masu rajin kare demokradiyya don ceto demokradiyyar kasar
 • Shugaban kasa ya magance matsalar rashin aikin yi da kuma talauci a kasar
 • Duka majalisoshin biyu sun nuna goyon baya ga shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara
 • Kuma ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar na 'yan sanda Najeriya Ibrahim Idris
 • Majalisa za ta dauki mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu.