Magidanci da iyalansa hudu sun mutu a Ogun

Hukumar 'yansnd ta ce ta soma bincikar lamarin Hakkin mallakar hoto Premuin times
Image caption Iyalin sun rasa rayukansu ne bayan da suka shiga sabon gidansu

Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun da ke kudancin Najeriya ta tabattar da mutuwar wani magidanci da matarsa da kuma 'ya'yansa uku bayan sun tare a sabon gidansu da ke garin Sagamu.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ya shaida wa BBC ewa kawo yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.

Sai dai rahotanni sun ce ana kyautata zaton feshin wani maganin da aka yi ne a sabon gidan ya yi sanadiyyar mutuwarsu.

Wani na kusa da iyalan ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Najeriya (NAN) cewa sun rika jin wari sosai bayan kwana daya da iyalan suka shiga sabon gidan.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka