Tarin makamai sun tarwatsa wani masallaci a Bagadaza

Iraqis inspect the aftermath of explosions that destroyed a mosque in Baghdad's Sadr City district (7 June 2018) Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masallacin da makaman suka tarwatsa na karkashin ikon malamin Shi'a Moqtada Sadr ne

Akalla mutum 17 suka rasa rayukansu kuma mutum 80 suka samu raunuka bayan da wasu makamai masu fashewa suka tarwatsa wani masallaci a birnin Baghdad na kasar Iraki.

Gwamnati ta ce fashewar ta auku ne a daren Laraba saboda adana wasu makamai da aka yi a cikin masallacin na 'yan Shi'a a yankin Sadr City.

Ba a bayyana ainihin inda aka ajiye tarin makaman ba, amma wasu jami'an tsaro sun ce a cikin masallacin aka boye su.

Masallacin na karkashin ikon magoya bayan malamin Shi'an nan Moqtada Sadr.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnati ta ce tana binciken yadda wannan bala'in ya auku

'Yan Iraki na duba baraguzan masallacin bayan da tarin makamai masu fashewa suka tarwatsa shi a yankin Sadr City na birnin Bagadaza.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai manya da kananan yara a cikin wadanda tashin bam din ya rutsa da su

Labarai masu alaka