Austriya ta rufe masallatai bakwai tare da korar limamai

A mosque in Austria, file pic, 13 Oct 17 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu ba a fadi sunayen masallatai bakwai din da za arufe ba

Austriya ta ce za ta rufe masallatai bakwai tare da korar limaman da ta ce wasu kasashe na daukar nauyinsu.

Shugaban gwamnatin kasar Sebastian Kurz, ya ce an dauki matakin ne don magance "musulunci mai tafe da siyasa."

Ana zargin wasu masallatan da cewa suna da alaka da kasar Turkiyya.

A watan Afrilu ne wasu hotuna suka bayyana da ke nuna yara sanye da inifom din sojojin Turkiyya suna kwaikwayon Yakin Duniya na Daya, Gallipoli.

Ofishin shugaban Turkiyya ya kira matakin na Austiya a matsayin "Kyamar musulmai, da nuna wariyar launin fata da kuma nuna bambanci."

Mai magana da yawun shugaban kasar

Gwamnatin Austriya ta ce ana bincikar limamai 60 daga cikin 260 na kasar, kuma 40 daga cikinsu 'yan wata kungiyar musulmai ce ta ATIB, da ke da alaka da gwamnatin Turkiyya.

An gudanar da kwaikwayon yakin duniya na Gallipoli din ne a wani masallaci na wata kungiya Grey Wolves ta 'yan Turkiyya, a yankin Vienna-Favoriten. Kungiyar na da rassa a kasashe da dama.

Kafafen watsa labaran Austriya sun ruwaito cewa yaran da suka yi kwaikwayon tamkar sun mutu an kuma rufe su da tutucin Turkiyya. An kuma ga wasu hotuna da yaran ke yin gaisuwa irin ta Grey Wolves a masallacin.

Sa-in-sar Austriya da Turkiyya

A ranar Juma'a ce shugaban gwamnatin Austriya Mista Kurz ya ce: "Ba ma maraba da da duk wata al'umma ta daban, da cakuda siyasa da musulunci da kuma tsattsauran ra'ayi a kasarmu."

A yakin neman zaben da Mista Kurz ya yi a bara, ya fito karara ya nuna damuwarsa a kan 'yan ci rani da hadin kan musulmai.

Mr Kurz yana so Tarayyar Turai ta yi watsi da bukatar Turkiyya ta neman zama mamba a tarayyar - matakin da ya dugunzuma Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

A watan Mayun shekarar 2017 wannan bacin ran ya sa Turkiyya ta hau kujerar na-ki kan hadin kan Nato da Austriya.

Matakin ya kawo cikas ga ayyukan hadin gwiwar Nato da kasashe 41. Turkiyya dai babbar mai taka rawa ce a ayyukan Nato.

Hukumomin Austriya na yin aiki da wata kungiyar musulmai da ake kira IGGO domin gano masallatai da limaman da ake zargin su da tsaurin ra'ayin addini ko kuma alaka da wasu kasashen.

Uku daga cikin masallatan da za a rufe a birnin Vienna suke, biyu kuma a jihar Upper Austria yayin da daya kuma yake Carinthia.

Labarai masu alaka