Falasdinawa na zanga-zanga domin zagayowar ranar Kudus

The weekly protests along the Gaza-Israel border fence have been taking place since March Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Faasdinawa ke gudanar da zanga-zanga a kan iyakar Gaza da Isra'ila

Dubban 'yan Falasdinu sun taru a kusa da iyakar Gaza da Isra'ila domin tunawa da Ranar Birnin Kudus.

Ma'aikatan jinya sun ce an jima akalla mutum 100 rauni - kuma da yawansu na cikin wani mawuyacin hali.

Kungiyar Hamas wadda ita ce ke iko da yankin na Gaza na jawo hankalin mutane su fita zuwa wajen zanga-zangar.

Mutane sun fara taruwa ne bayan sallar Jumma'a domin karrama Jumma'a ta karshe a watan Ramadan. Falasdinawa sun rika amfani da amsakuwa suna bayyana cewa Birnin Kudus mallakinsu ne.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Abubuwa da Falasdinawa ke harbawa cikin Isra'ila sun kone fiye da eka 2,250 na daji a Isra'ila

Mun kuma ga masu zanga-zanga na kiona tayoyin mota. Sun kuma rika daura bama-bamai na fetur, inda suke aikawa da su cikin Isra'ila, kuma sun yi sanain kona gidaje masu dama a cikiin Israilar.

Dakarun Israila sun rika mayar da martani da hayaki mai sa hawaye, sannan sun rika yin harbi domin kora masu zanga-zanga daga bakin iyaka.

Israila ta ce ta na yin harbi ne domin ta kare kanta da iyakokin kasarta.

Su kuma Falsdinawa sun ce suna zanga-zanga ne don kwato filayensu da a halin yanzu ke cikin Israila.

Shugabannin Falasdinawa sun ce yanzu aka fara wannan tada kayar bayan, domin ba za su daina ba har sai sun cimma nasara.

Labarai masu alaka