Trump da Kim na dab da kafa tarihi a Singapore

Kim Jong-un and Donald Trump arrive separately in Singapore on 10 July 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters/Getty Images
Image caption Shugabannin sun isa Singapore, kuma tsakaninsu awoyi kadan ne

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya isa Singapore domin halartar taron koli tsakaninsa da Shugaba Trump na Amurka.

Shugabanni biyu za su tattauna kan batun makaman nukiliyar Koriya ta Arewa, da samar da dauwamammen zaman lafiya a yankin Koriya.

Shi ma shugaba Trump ya isa Singapore daga baya, kuma shugabannin biyu na son kafa tarihi a lokacin da suka hadu a karon farko ranar Talata,

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya isa Singapore a wani jirgin saman China, inda ministan harkokin waje na Singapore ya tarbe shi, kafin ya gana da Firayiministan kasar.

Wannan babbar dama ce ga shugaban na Koriya ta Arewa, domin yana da yekinin sauyawa daga yadda duniya ke kallonsa a matsayin mai mulkin kama karya da kuma mai son tada rikici.

Yana son ya zama mai fada aji a siyasar duniya da diflomasiyya.

Image caption Taswirar wajen da ganawar shugabannin biyu za ta kasance

Yana kuma fatan wannan ne lokacin da kasarsa za ta sami karbuwa a cikin kasashen duniya.

Babban batun da za a tattauna a kai shi ne na mallakar makan nukiliyar kasar - ko zai yarda ya mika su domin a dage ma kasarsa jerin takunkuman karya tattalin arziki.

Shi ma shugaba Trump na Amurka na fatan wannan taron zai ba shi damar cimma yarjejeniyar da za ta ama irinta ta farko a duniya.

Amma duk da haka, Mista Trump yayi kasa-kasa da fatan da yake yi na cimma wata kwakkwarar yarjejeniya a haduwarsu ta farko.