Hotunan yadda Musulmai ke shirin bikin Sallah a fadin duniya

Ga wasu zababbun hotuna da BBC ta wallafa muku, da ke nuna yadda musulmai ke shirye-shiryen gudanar da karamar sallah a fadin duniya, bayan kammala azumin watan Ramadan.

Musulamn Indonesiya na yin bulaguro don sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fasinjoji na ta fitowa daga cikin wani jirgin ruwa yayin da ya isa tasar jiragen ruwa ta Surabaya da ke kasar Indonesiya. Fasinjojin dai na yin bulaguro ne zuwa garuruwansu don gudanar da bikin Sallah Karama bayan kammala azumin Ramadan. A ko wacce shekara, manyan biranen da ke Indonesiya - kasar da ta fi ko wacce yawan musulmai kan zama tamkar ba mutane, saboda yadda mafi yawan mazaunansu kan tafi kauyukansu don yin shagalin sallah a can tare da danginsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A Indiya kuwa nan hoton wata mata ce a garin Ramganj Bazar na Jaipur da ke jihar Rajasthan, take busar da wani nau'in abincin gargajiya mai kama da taliyar Hausa mai suna 'Vermicelli' ko 'Sewaiyan' don sayar wa ga masu bukata, wadanda za su dafa shi a ranar sallah.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A Pakistan kuwa, mata ne ke ta rububin zuwa shagunan sayar da gwala-gwalai da kayan kawa, don sayen kayan adon da za su gwamgwaje da su ranar sallah.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yemenis buy sweets and nuts at a market in Sanaa on June 10, 2018, as Muslims prepare to celebrate Eid al-Fitr on the occasion of the holy month of Ramadan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan kasar Bangladesh da dama su na yin bulaguro zuwa kauyukansu daga birane, don yin bikin sallah tare da 'yan uwansu. Wannan hoton na nuna wasu yara da ke tafiya tare da iyayensu zuwa garinsu a cikin jirgin kasa daga birnin Dhaka. Tashar jirgin kasa ta Dhaka ta yi cikar kwari a kwanakin karshe na Ramadan inda matafiya ke ta kara-kaina.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yayin da a wasu kasashen ake rububin ayen kayan sawa na adon sallah, a Malaysia kuwa mata ne ke sayen darduma wacce za su yi shimfidar adon sallah da ita a gidajensu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu 'yan Syria da dama na koma wa kasarsu daga Turkiyya don gudanar da bikin sallah. Sun bi ta kan iyakar Cilvegozu ne a Reyhanli Hatay. A kalla 'yan Syria 70 ne suka bi ta Cilvegozu don isa garinsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shirye-shiryen sallah a Afghanistan ya kankama, amma kasuwar masu sayar da kayan marmari da alawa ce ta fi ci sosai,, domin su ne abubuwan da 'yan kasar suka fi yin bikin sallah da su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu iyalai a Falasdinu su na ta aikin soya kayan kwalam da ake yi da dabino, a gidansu da ke yankin Khan Yunis, a kudancin Zirin Gaza.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Motocin matafiya masu yin bulaguro zuwa garuruwansu don yin karamar sallah sun cika hanya makil, a kan titin Batang-Semarang da ke birnin Java, a ranar 12 ga watan Yunin 2018. Motocin sun jawo cunkoso sosai a titin.

Bayanan hoto,

Wata mata 'yar Thailand tana gwada wa wani yaro hula don ganin ko ta yi masa daidai don a saya masa ta adon sallah. Wannan duk yana cikin shirye-shiryen sallah da ake gudanarwa ne a garin Narathiwat da ke yankin kudancin kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane na ta sayen kayan sallah a wata kasuwar dare da ke wajen birnin Kuala Lumpur na Malaysia, domin gwangwajewa da su a yayin bikin sallah da ake sa ran yi ranar Juma'a ko Asabar.