'An kashe mutum 31 a Zamfara'

Zamfara

Wasu 'Yan bindiga sun kashe mutum 31 a hare-haren da suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamafara.

Hare-haren sun shafi kauyuka hudu da ke cikin yankin Kiyawa da Gora a karamar hukumar Birnin Magaji.

Alhaji Ibrahim Dan madamin Birnin Magaji kuma kwamishin kasafi da tsare-tsare a Zamfara ya shaidawa BBC cewa an kai kai hare-haren ne kauyukan Illojiya da Madambaji da Sabon Garin Madambaji da Oho da kuma Dutsen wake.

"Kauyen Dutsen Wake kawai an kashe mutum 18, a kauyen Oho mutum 8, a kauyen Illojiya mutum biyu, a Madambaji mutum biyu, yayin da Sabon garin Madambaji aka kashe mutum daya," in ji shi.

Sai dai kuma kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara DSP Muhammad Shehu ya shaidawa BBC cewa mutum 10 ne aka kashe a hare haren da aka kai a Dutsen Wake da kuma Oho.

Ya ce rundunar 'yan sanda ta samu labarin harin amma ko da jami'anta suka isa yankin har maharan sun gudu.

Wannan al'amari na zuwa bayan kisan mutane sama da 50 a cikin mako daya a Zamfara, inda aka kashe mutum 23 a kauyen Zaloka a karamar hukumar Anka da kuma mutum 27 da aka kashe a yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar mulki ta Maradun.

Daruruwan mutane aka kashe a Zamfara a tsawon shekaru shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.

Yawaitar kashe-kashen da ake samu kusan a kullum ya tursasawa daruruwan mutanen Zamfara yin kaura zuwa makwabtan jihohi.