APC ta zargi Okorocha da bata wa shugabanninta suna

APC

Asalin hoton, Getty Images

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zargi gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda shi ma dan jam'iyyar ne, da bata wa shugabanninta suna.

Zargin na jam'iyar na cikin wata sanarwar da kakakin jam'iyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.

Jam'iyyar ta shawarci gwamnan ya yi aiki tare da sabbin shugabannin jam'iyyar da aka zaba a jiharsa tare bin hanyar sulhu.

Mista Okorocha dai ya zargi jam'iyyarsa ta APC da kin bin umarnin kotu wajen rantsar da sabon shugaban jam'iyyar na jihar Imo bayan ce-ce-ku-ce da aka yi akan zabensa.

Sai dai kuma jam'iyyar ta ce ba ta samu wani umarnin kotu ba game da taron jam'iyyar da ya samar da sabon shugaban.

Asalin hoton, Getty Images

Sanarwar ta ce: "Cikin 'yan makwannin nan, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, yana bata wa jam'iyyarmu da shugabanninta suna a ko wace rana."

Sanarwar ta kara da cewa, kusan babu wata ranar da gwamnan ba zai caccaki shugaban jam'iyyar APC na kasa, Chief John Odigie-Oyegun ba, da sauran shugabannin jam'iyyar kan zaben shugabanni da aka yi a jihar Imo.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"A cikin wata talla da aka wallafa a jaridar Daily Trust, ranar 11 ga watan Yunin 2018 mai taken: 'A bar gaskiya ta yi magana da kanta' wadda sanannen makusancin gwamna Okorocha, Ireagwu Obioma, mai kiran kansa sakataren riko na jam'iyyar APC a Imo, an yi ikirarin wasu abubuwan da ba gaskiya ba game da jam'iyyar."

Sanarwar ta ce jam'iyyar ta gudanar da taronta na jihar duk da cewar ta sami takardar umarnin da ta hana ta yin hakan daga kotu.

Sai dai kuma jam'iyyar ta ce ba haka ba ne, tana mai cewar hukuncin kotun da gwamnan yake yayatawa bai mara wa abun da yake ikirari baya ba.

Zaben shugabannin APC a mazabu da kananan hukumomi da aka gudanar a jihohin da jam'iyyar ke mulki ya bar baya da kura.

Rikicin cikin gida na jam'iyyar ya yi tasiri sosai a zabukan inda a wasu jihohi wasu 'ya'yan jam'iyyar suka ware suka gudanar da nasu zaben na daban.

Duk da cewa APC ta ce ta yaba da yadda aka gudanar da zaben na shugabanninta a sassan kasar, amma masharhanta na ganin sabanin da ya biyo baya babban kalubale ne ga jam'iyyar.

Ana ganin idan har jam'iyyar ba ta sasanta tsakanin 'ya'yanta ba, to wasu daga cikinsu da suke ganin an saba ma su na iya ficewa zuwa wata jam'iyyar adawa.