Zolaya ce a kira gwamna babban jami’in tsaro - Gwamnan Zamfara

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar

Latsa hoton da ke sama domin sauraren hirar gwamnan Zamfara da Awwal Janyau

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar ya ce mukamin babban jami'in tsaron jiha ga gwamna batu ne da ya kamata majalisar dokokin Najeriya ta diba.

Gwamnan wanda jiharsa ke fama da matsalar tsaro ya shaidawa BBC cewa zai kai kudirin gaban majalisa, "ko dai a cire mukamin ko kuma a kara wa gwamna karfi."

"Zaloya ce a kira gwamna da mukamin babban jami'in tsaro domin bai iya hukuntawa ko dauka da korar karamin jami'in tsaro" in ji shi.

Ya ce doka ba ta ba gwamna dama ba, sai dai ya kara da nashi kokari ga wanda gwamnatin Tarayya ke yi.

Zamfara ta shafe shekaru kusan takwas tana fama da matsalar 'yan fashi da barayin shanu da sace-sacen mutane.

Gwamnan jihar ya ce yana jagorantar wani sabon shiri na tunkarar matsalar tsakanin al'ummar jihar ta hanyar tattaunawa da masarautun gargajiya domin gano bakin zaren.

Daruruwan mutane ne aka kashe a hare-haren 'yan bindiga a Zamfara.

Yawaitar kashe-kashen da ake samu kusan a kullum ya tursasawa daruruwan mutanen Zamfara yin kaura zuwa makwabtan jihohi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka