Afirka ta Kudu: An sake kai hari a masallaci

Cyril Ramaphosa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu

Mazauna birnin Cape Town na cikin tashin hankali bayan wani harin da wani ya kai kan masu ibada a wani masallaci.

Harin yayi sanadin mutuwar mutum uku har da shi maharin.

Wannan harin ya auku ne a daidai lokacin da masu ibadah ke shirin gudanar da sallar asuba da misalin karfe 3 na asuba a birnin Cape Town.

Ana ganin maharin ya shiga masallacin ne, inda ya tambayi wasu su nuna masa hanyar zuwa wani wuri, amma kuma babu sanannen ciki sai ya daba ma wasu masallata su biyu hari da wata wuka, kana ya bar wasu mutum uku da raunuka.

Da jami'an tsaro suka isa wurin, sun ce maharin yana da shekara 30 da wani abu, kuma ya ki yarda ya mika makamin da yake rike da shi.

Ya kai ma dan sanda hari, amma ya harbe shi. Wadanda suka gane ma idansu lamarin sun ce wukar babba ce irin wadda aka yi amfani da ita a fim din Rambo ce.

Hukumar da ke kula da al'amuran Musulmai a kasar ta yi tir da harin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce ta kadu kwarai da jin yadda aka kai wannan harin na rashin imani.

Wannan harin dai ya auku ne kasa da wata daya da aka kai wani hari a wani masallacin da ke garin Durban a yankin KwaZulu-Natal.

A wancan harin, wasu mahara uku ne suka kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya, kuma mutum biyu sun sami rauni.

Labarai masu alaka