Melania Trump ta soki mijinta kan bakin haure

A two-year-old Honduran asylum seeker cries as her mother is searched and detained near the US-Mexico border on 12 June 2018 in McAllen, Texas. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hotunan yadda ake raba iyaye da kananan yaransu a kan iyakokin Amurka sun janyo wa gwamnatin kasar bakin jini

Matar shugaban Amurka Melania Trump ta fito fili ta soki shirin gwamnatin Amurka na raba iyaye da 'ya'yansu idan an kama su da laifin shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Melania Trump ta ce "na ki jinin yadda ake raba yara da iyayensu", kuma ta na son ganin an samar da wata sahihiyar hanya ta tunkarar matsalar.

Kalamanta sun biyo bayan karuwar damuwa da Amurkawa ke nunawa kan yadda shugaba Donald Trump ke aiwatar da shirin nasa mai suna "zero tolerance" wajen yaki da bakin haure.

Laura Bush, matar tsohon shugaban Amurka George W Bush ma ta soki lamirin shirin, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ke cike da keta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Melania Trump ta yi kira ga 'yan siyasar kasar da su hada kai domin kawo karshen matsalar

A 'yan makonnin da suka gabata, an raba iyalai kimanin 2,000 da 'ya'yansu bayan da gwamnatin kasar ta tashi tsaye wajen yaki da masu tsallaka iyakokin Amurka ta barauniyar hanya.

A kan tsare dukkan balagaggen da aka kama na kokarin shiga kasar ko da yana da dalilin yin haka, kuma zai fuskanci matakin shari'a.

Labarai masu alaka