An samu tashin gobara a kasuwar Azare

Gobarar ta fi shafar bangaren kayayyakin abinci, tufafi da sauran kayayyakin masarufi. Hakkin mallakar hoto Sabbar Aminu Azare
Image caption Gobarar ta fi shafar bangaren kayayyakin abinci, tufafi da sauran kayayyakin masarufi.

Rahotanni daga garin Azare da ke jihar Bauchi a Najeriya na cewa an samu tashin gobara a babbar kasuwar garin.

Gobarar dai kawo yanzu ta yi sanadiyar hasarar dukiya mai dimbin yawa kamar yadda mazauna garin suka shaida wa BBC.

Hakkin mallakar hoto Sabbar Aminu Azare

Wakilin BBC, Ishaq Khalid ya ce har yanzu ba a gano musababin gobarar ba, sai dai ma'aikatan kwana-kwana na kokarin gani yadda za su kashe gobarar da ke ci tun daran jiya Litinin.

Gobarar ta fi shafar bangaren kayayyakin abinci, tufafi da sauran kayayyakin masarufi.

Kuma kawo yanzu babu rahotanni asarar rayuka.

Tashin Gobarar na zuwa ne adai-dai lokacin da al'ummar jihar ke jimamin aukuwar iftila'in ruwan sama mai karfin gaske da ya haifar da asarar dimbim dukiya da gidaje.

Hakkin mallakar hoto .

Labarai masu alaka