Yadda Donald Trump ke raba 'ya'yan 'yan ci-rani da iyayensu

Bayanan bidiyo,

Yadda 'ya'yan 'yan ci-ranin Amurka ke kukan an raba su da iyayensu

An saki wasu muryoyin yaran 'yan ci-ranin Amurka da aka nada suna kuka sakamakon raba su da iyayensu, yayin da Shugaba Donald Trump ke ci gaba da bujirewa sauya dokokin 'yan ci-rani.

Kusan 'ya'yan 'yan ci-rani 2,000 ne aka raba da iyayensu a watannin da suka gabata, bayan da iyayensu su ka yi kokarin shiga Amurka ta kan iyaka ba tare da izini ba.

Mista Trump ya ce ba zai bari Amurka ta zama sansanin "'yan ci-rani ba."

Babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ya ce ba za a amince da dokar ba.

Wata kafar watsa labarai mai binciken kwaf a Amurka ProPublica ce ta saki muryoyin a ranar Litinin, kuma an ce an nadi kukan ne a wani sansani na hukumar kwastam da tsaron iyaka ta Amurka.

A ciki, an ji muryoyin yara da dama 'yan yankin Tsakiyar Amurka da aka raba da iyayensu da ake tsammanin 'yan tsakanin shekara hudu zuwa goma ne, suna kuka da shessheka tare da kiran sunan iyayensu.

A ciki an ji muryar wani jami'i mai kula da kan iyaka ya na cewa: "Mun samu kayan kida a nan. Abun da babu kawai shi ne wanda zai buga."

Babban jami'in UNHCR Filippo Grandi, ya shaida wa BBC cewa ba za a amince da dokar Trump ta korar 'yan ci-rani ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matsayin Donald Trump kan 'yan ci-rani na haifar da ce-ce-ku-ce a kasar

Ya ce: "Ba daidai ba ne a raba yara da iyayensu a ko wanne irin yanayi musamman a lokacin da mutane ke cikin tsanani kamar gujewa rikici ko cin zarafi, kamar yadda yake faruwa a Tsakiyar Amurka.

"Don haka mu na shawartar gwamnatin Amurka cewa ba wannan ce hanyar da ya kamata ta bi wajen daukar mataki ba," in ji Musa Grandi.

A ranar Litinin ne Mista Trump ya ce Amurka ba za ta zama sansanin 'yan ci-rani ba.

"Idan aka kalli abun da ke faruwa a Turai da sauran wurare, ba za mu bar hakan ya faru a Amurka ba. Ba zan bari ba."

Shugaban dan jam'iyyar Republican ya zargi 'yan jam'iyyar Democrat da cewa sun ki zuwa teburin sasantawa kan dokar ci-rani.

Mece ce dokar?

Asalin hoton, Administration for Children and Families at HHS

Bayanan hoto,

Hoton farko da aka saki a hukumance da ke nuna birnin da ake kafa tantuna don ajiye 'ya'yan 'yan ci rani a Texas

Kusan yara 2,000 aka raba da iyayensu a kan iyaka daga tsakanin tsakiyar watan Afrilu zuwa karshen watan Mayu.

Daga cikin dokar Shugaba Trump din akwai kama da kuma tuhumar wadanda aka kama su na shiga Amurka ba bisa ka'ida ba da laifi, har da masu neman mafaka.

Al'amarin ya jawo an raba yara da iyayensu, da ba su da laifin komai.

A sakamakon haka, an ajiye daruruwan yara a cibiyoyin tsare mutane da dama.

Wasu hotunan sansanonin sun nuna yadda aka kange yara a cikin keji.

A yanzu haka dai babu isasshen wajen da za a ajiye yaran.

Jami'ai sun kuma sanar da shirin gina birnin da za a kafa tantuna da za su iya daukar daruruwan yara a dajin Texas inda yanayin zafin wajen ke kai wa digiri 40 a ma'aunin salshiyas.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jama'a da dama ne ke kokarin shiga Amurka ba bisa ka'ida ba musamman daga yankin Tsakiyar Amurka

Wa ke sukar dokar?

Jam'iyyar Democrat da wasu 'yan jam'iyyar Republican ta Mista Trump sun yi Allah-wadai da mulkinsa.

Al'amarin ya jawo suka mai tsanani daga matarsa Melania Trump, wacce a karshen makon da ya gabata ma ta ce ta "tsani ganin an raba yara da iyayensu."

Ita ma tsohuwar 'yar takarar shugabar kasa ta Democrat Hillary Clinton ta ce abun da Mista Trump ke ikirari cewa raba iyaka na cikin doka, "karya ce tsagwaronta."

Sai dai da dama daga cikin 'yan majalisar dokoki na Republican ba su soki Trump kan dokar ba.

Karanta karin wasu labarai kan Mexico

Bayanan bidiyo,

Yadda 'ya'yan 'yan ci-ranin Amurka ke kukan an raba su da iyayensu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An saki wasu muryoyin yaran 'yan ci-ranin Amurka da aka nada suna kuka sakamakon raba su da iyayensu, yayin da Shugaba Donald Trump ke ci gaba da bujirewa sauya dokokin 'yan ci-rani.

Kusan 'ya'yan 'yan ci-rani 2,000 ne aka raba da iyayensu a watannin da suka gabata, bayan da iyayensu su ka yi kokarin shiga Amurka ta kan iyaka ba tare da izini ba.

Mista Trump ya ce ba zai bari Amurka ta zama sansanin "'yan ci-rani ba."

Babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ya ce ba za a amince da dokar ba.

Wata kafar watsa labarai mai binciken kwaf a Amurka ProPublica ce ta saki muryoyin a ranar Litinin, kuma an ce an nadi kukan ne a wani sansani na hukumar kwastam da tsaron iyaka ta Amurka.

A ciki, an ji muryoyin yara da dama 'yan yankin Tsakiyar Amurka da aka raba da iyayensu da ake tsammanin 'yan tsakanin shekara hudu zuwa goma ne, suna kuka da shessheka tare da kiran sunan iyayensu.

A ciki an ji muryar wani jami'i mai kula da kan iyaka ya na cewa: "Mun samu kayan kida a nan. Abun da babu kawai shi ne wanda zai buga."

Babban jami'in UNHCR Filippo Grandi, ya shaida wa BBC cewa ba za a amince da dokar Trump ta korar 'yan ci-rani ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matsayin Donald Trump kan 'yan ci-rani na haifar da ce-ce-ku-ce a kasar

Ya ce: "Ba daidai ba ne a raba yara da iyayensu a ko wanne irin yanayi musamman a lokacin da mutane ke cikin tsanani kamar gujewa rikici ko cin zarafi, kamar yadda yake faruwa a Tsakiyar Amurka.

"Don haka mu na shawartar gwamnatin Amurka cewa ba wannan ce hanyar da ya kamata ta bi wajen daukar mataki ba," in ji Mista Grandi.

A ranar Litinin ne Mista Trump ya ce Amurka ba za ta zama sansanin 'yan ci-rani ba.

"Idan aka kalli abun da ke faruwa a Turai da sauran wurare, ba za mu bar hakan ya faru a Amurka ba. Ba zan bari ba."

Shugaban, dan jam'iyyar Republican ya zargi 'yan jam'iyyar Democrat da cewa sun ki zuwa teburin sasantawa kan dokar ci-rani.

Mece ce dokar?

Asalin hoton, Administration for Children and Families at HHS

Bayanan hoto,

Hoton farko da aka saki a hukumance da ke nuna birnin da ake kafa tantuna don ajiye 'ya'yan 'yan ci rani a Texas

Kusan yara 2,000 aka raba da iyayensu a kan iyaka daga tsakanin tsakiyar watan Afrilu zuwa karshen watan Mayu.

Daga cikin dokar Shugaba Trump din akwai kama da kuma tuhumar wadanda aka kama su na shiga Amurka ba bisa ka'ida ba da laifi, har da masu neman mafaka.

Al'amarin ya jawo an raba yara da iyayensu, da ba su da laifin komai.

A sakamakon haka, an ajiye daruruwan yara a cibiyoyin tsare mutane da dama.

Wasu hotunan sansanonin sun nuna yadda aka kange yara a cikin keji.

A yanzu haka dai babu isasshen wajen da za a ajiye yaran.

Jami'ai sun kuma sanar da shirin gina birnin da za a kafa tantuna da za su iya daukar daruruwan yara a dajin Texas inda yanayin zafin wajen ke kai wa digiri 40 a ma'aunin salshiyas.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jama'a da dama ne ke kokarin shiga Amurka ba bisa ka'ida ba musamman daga yankin Tsakiyar Amurka

Wa ke sukar dokar?

Jam'iyyar Democrat da wasu 'yan jam'iyyar Republican ta Mista Trump sun yi Allah-wadai da mulkinsa.

Al'amarin ya jawo suka mai tsanani daga matarsa Melania Trump, wacce a karshen makon da ya gabata ma ta ce ta "tsani ganin an raba yara da iyayensu."

Ita ma tsohuwar 'yar takarar shugabar kasa ta Democrat Hillary Clinton ta ce abun da Mista Trump ke ikirari kan batun iyaka na cikin doka, "karya ce tsagwaronta."