Atiku ya ‘daura’ damarar tunkarar zaben 2019

Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari
Bayanan hoto,

Atiku ya goyi bayan Buhari a zaben 2015 amma sun raba gari daga bisani

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma mai neman jam'iyyar adawa ta PDP ta tsayar da shi takara a zaben 2019, ya fara rangadin wasu jihohin kasar a yankurinsa na doke Shugaba Muhammadu Buhari.

Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Ekiti, inda ya gana da Gwamna Ayo Fayose da sauran jami'an gwamnati da shugabannin jam'iyyar a jihar.

Duka Mista Fayose da Atiku sun bayyana aniyyarsu ta neman yi wa PDP takara domin kawar da gwamnatin APC, wacce suka ce ta gaza wurin ciyar da kasar gaba.

Sanarwar da jagoran yakin neman zaben Atiku Abubakar, Gbenga Daniel, ya fitar ta ce tawagar za ta ziyarci birnin Yenagoa na jihar Bayelsa ranar Talata domin ci gaba da rangadin.

Ta kara da cewa Atiku zai sake kai ziyara jihar Rivers, inda zai shafe kwana biyu yana tattaunawa da jami'an gwamnati da na jam'iyya, sannan ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Nyesom Wike ya aiwatar.

A lokacin da yake Ekiti, Atiku ya nemi jama'ar jihar da su goyi bayan dan takarar jam'iyyar a zaben gwamna da za a yi a ranar 14 ga watan Yuli wato Kolapo Olusola.

"Daga nan kuma tawagar za ta garzaya jihohin Legas da Delta a ranakun 24 da kuma 26 ga watan Yuni," a cewar sanarwar.

A baya ma dai Atiku ya ziyarci Ekiti da Rivers, da Akwa Ibom da kuma Cross River inda ya gana da gwamnonin jihohin kafin fara azumin watan Ramadan.

A nan gaba kuma ana sa ran zai ziyarci jihohin Abia, Enugu, Ebonyi, Gombe da Taraba.

Masu sharhi na ganin jam'iyyar PDP na da kalubale a gabanta a wurin karbar mulki duk da cewa jam'iyyar APC mai mulki na fama da dimbin matsaloli.

Masu neman takara a PDP

  • Alhaji Atiku Abubakar
  • Ayo Fayose
  • Malam Ibrahim Shekarau
  • Sule Lamido
  • Ahmed Makarfi
  • Ibrahim Hassan Dan Kwambo (bai bayyana ba kawo yanzu)