Hotunan Gasar Cin Kofin Duniya a Rasha

Kalli wadansu hotuna da muka zabo daga gasar cin kofin duniya wanda aka fara a kasar Rasha a makon jiya.

A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tawagar kwallon kafar Rasha wadda ita ce mai masaukin baki ta doke ta Saudiyya da ci 5-0 a wasan farko a gasar kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ita kuwa tawagar kwallon kafa ta Brazil ta tashi kunnen doki 1-1 da kasar Switzerland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jamus, wadda ta lashe kofin duniya a shekarar 2014, ta yi rashin nasara ne a hannun tawagar kwallon kafa ta Mexico da ci 1-0

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Najeriya ta yi rashin nasara a hannun Croatia da ci 2-0, Super Eagles za ta buga wasa na gaba da Iceland da kuma Argentina kafin ta san matsayinta a gasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ita ma tawagar kwallon kafa ta Tunisiya ta yi rashin nasara a hannun Ingila da ci 2-1

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wadansu magoya bayan tawagar kwallon kafa ta Colombia gabanin karawarsu da kasar Japan a ranar Talata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Koda yake babban dan wasan kasar Masar, Mohamed Salah bai buga karawar da tawagar kwallon kafa ta Uruguay ta yi nasara da ci 1-0 ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalin wasa Joel Aguilar yana sake kallon wani bangaren alkalanci a talabijin gabanin ya ba da bugun fenariti ga kasar Sweden a wasansu da Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tawagar kwallon kafa ta Iran ta doke ta Morocco da ci 1-0

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Magoya bayan tawagar kwallon kafar Japan lokacin wasan da kasar ta doke Colombia da ci 2-1