An hana jami'an tsaro amfani da shafukan sada zumunta

android Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Haka kuma an hana jami'an yin amfani da wayoyin hannu na Android

Gwamnatin Kamaru ta haramtawa jami'an tsaro na Jandarma amfani da shafukan sada zumunta irin su WhatsApp da Facebook da Twitter.

Karamin ministan tsaro na kasar wanda ya sanya dokar, ya kuma nemi da jami'an tsaron su soke zaurukan mahawarori da na kulla zumunta da suka bude a dukkanin shafukan sada zumunta.

Haka kuma an hana jami'an yin amfani da wayoyin hannu na Android.

Wannan hukuncin ya biyo bayan abin da kakakin Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya kira bata wa jami'an tsaro suna ba tare da hujja ba.

Kazalika an kuma bukaci daidaikun jami'an tsaron da suka bude shafukan karan-kansu a Facebook da Twitter da WhatsApp da hakan ke tantance su a matsayinsu na jami'an tsaro da su rufe su.

Karamin ministan ya dauki wannan matakin ne domin takaita bayyana wasiku, da kuma wasu tsare-tsare na sirri da Gwamnati take yi daga fadar Shugaban kasa zuwa ma'aikatar tsaro.

Baya ga haka kuma da akwai yunkurin wanke jami'an tsaron ga zarge-zargensu da ake yi na cin zarafi da gallazawa da tauye hakkin fararen hula da suke yi, a tarin faya-fayan bidiyo da jama'a suke yin musaya a tsakaninsu.