An harbe wani dan majalisa a Afirka ta Kudu

Sibusiso Radebe

Asalin hoton, Mpumalanga News

'Yan bindigsa sun harbe wani dan majalisa na jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu har lahira.

Sibusiso Radebe ya rasa ransa ne a wani lamari da ake yi wa kallon aikin 'yan fashi da makami ne.

An harbe shi ne a ka da kuma kafa bayan da maharan suka bukaci wayar salularsa, kamar yadda wani dan uwansa Lungile Dube ya shaida wa kafar watsa labarai ta Mpumalanga News.

Lamarin ya faru ne a birnin Roodepoort a cibiyar kasuwanci ta kasar da ke Gauteng.

Wani dan jarida da ke yankin ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter kamar haka:

"An harbe dan majalisar ANC Sibusiso Radebe har lahira a Roodepoort".