Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin bana

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Bashir Ahmed/Twitter
Image caption Muhamnmadu Buhari, wanda aka zaba a 2015 bisa alkawarin yaki da cin hanci da samar da ayyukan yi, na neman wa'adi na biyu a zaben 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na 2018 a fadarsa da ke Abuja.

A tsakiyar watan Mayu ne majalisun dokokin kasar suka amince da kasafin kudin, wanda ya kai naira tiriliyon 9.1, wata shida bayan da shugaban ya gabatar musu da shi.

Hakazalika 'yan majalisun sun kara fiye da naira miliyan 500 a kan adadin kasafin na tiriliyon 8.6.

'Yan majalisar sun kuma kara adadin farashin man fetur da gwamnati ta tsara kasafin a kai daga dala 45 zuwa 51, suna masu cewa hakan ya zama dole saboda ganin yadda farashin man ya tashi a kusuwannin duniya.

'Shugaban kasa bai ji dadin sauye-sauyen ba'

Cikin sauye-sauyen da majalisar dokokin kasar ta yi a kasafin na bana, wadanda kuma shugaban kasar ya nuna rashin jin dadinsa sun hada da rage biliyoyin naira da aka ware don yi wasu manyan ayyuka.

Ciki kuwa har da aikin tashar wutar lantarki na Mambila da gada ta biyu ta kogin kwara da gina wasu tituna da layin dogo da shirin gina gidaje na gwamnatin tarayya da wasu ayyuka a bangaren kiwon lafiya da samar da tsaro.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, ba tare da tuntubar bangaren zartarwa ba, majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14, wanda a yasa a yanzu ta ke da kasafin sama da naira biliyan 139 maimaikon naira biliyan 125 da aka ware mata tun da fari.

Sannan an kara kudade don gina wasu sabbin tituna kimanin 70 a karkashin ma'aikatar makamashi da ayyuka da samar da gidaje.

Shugaban kasar dai ya ce yana da aniyar gyara wasu muhimman sauye-sauyen da aka yi ta hanyar gabatar da wani kwarya-kwaryan kasafi ga majalisar ko kuma yin gyara ga wannan kasafin.

Martanin Majalisa

A nata bangaren, majalisar dai ta ce ta kara kasafin ne daga sama da naira tiriliyan takwas zuwa fiye da naira tiriliyan tara saboda hasashen cewa farashin danyen mai zai iya kai wa dalar Amurka 51 kowane ganga, ba dala 45 da shugaban kasar ya sanya ba a kasafin da ya gabatar a watan Nuwambar shekarar 2017.

Kuma majalisar ta amince da kasafin ne bayan shafe watanni shida tana aiki akansa, inda daga bisani ta yi karin fiye da naira biliyan dari biyar a kan kasafin kafin ta mika wa fadar shugaban kasar.

Tsokacin masana tattalin arziki

Wani masanin tattalin arziki Farfesa Nazifi Darma, ya shaida wa BBC cewa rashin sanya hannu kan kasafin kudin a kan lokaci yana yin tasiri ga ci gaban habakar tattalin arzikin kasar.

"Gwamnati na da tasiri matuka kan tattalin arzikin Najeriya, a don haka jinkirin da ake samu babu shakka zai shafi tattalin arzikin kasar," a cewar Farfesa Darma, wanda malami ne a jami'ar Abuja.

Sai dai malamin ya yaba da yadda aka ware kudade ga fannin noma, yana mai cewa hakan zai taimaka wuirn samar da ayyukan yi.

Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa a hankali bayan da ya fuskanci mummunan koma-baya a shekarar 2016.

Shugaba Muhamnmadu Buhari, wanda aka zaba a 2015, bisa alkawarin yaki da cin hanci da samar da ayyukan yi, na neman wa'adi na biyu a zaben badi.

Sai dai wasu na sukar yadda ya fuskanci matsalar tattalin arzikin, duk da cewa yana bugar kirjin samun nasarori.

Haka kuma kasar ta yi fama da mummunan hauhawar farashin kayan masarufi a tsawon wannan lokaci.

Sharhi, Muhammad Kabir Muhammad, BBC Abuja

Alkaluma na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta Najeriya (wato National Bureau of Statistics ko NBS a takaice) ta fitar sun nuna cewa a watan Maris, kimar hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a Najeriya idan aka kwatanta da watan Fabrairu, daga kashi 14.33 cikin 100 zuwa kashi 13.34 cikin 100.

Wannan ne kuma wata na 14 a jere da kimar hauhawar ke raguwa.

"Wannan raguwar, a karo na 14 a jere tun daga watan Janairun 2017, ta nuna hauhawar ta ragu da kashi 0.99 cikin dari idan aka kwatanta da watan Fabrairun bana", in ji NBS.

Daga watan Fabrairun 2016 ne dai kimar hauhawar ta fara tashin gwauron zabi (lokacin da ta tashi daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu zuwa kashi 11.38 cikin dari) har ta kai matakin da aka yi shekara shida ba a kai makamancinsa ba a watan Janairun 2017, lokacin da ta kai kashi 18.72 cikin 100 (duba hoton da ke kasa).

Tattalin arzikin Najeriya a shekara uku da suka wuce

  • Mayu 2015: Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki
  • Fabrairu 2016: Farashin danyen man fetur ya fadi warwas zuwa kasa da $35 daga $115 a watan Yunin 2014
  • Fabrairu 2016: Kimar hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 11.38 cikin dari daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu
  • Afrilu 2016: A rubu'i na farko na 2016 kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi asarar sama da tiriliyan daya na Naira. Zuwa karshen shekarar kuma jimillar abin da ta yi asara ya tashi naira biliyan 604.
  • Yuni 2016: CBN ya karyar da darajar Naira
  • Agusta 2016: Tattalin Arzikin Najeriya ya durkushe a hukumance
  • Satumba 2017: Tattalin arzikin Najeriya ya farfado

Najeriya dai ita ce kasar da ta fi ko wacce arzikin danyen mai a Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen da suka fi arzikin man a duniya. Kuma tattalin arzikinta ya dogara ne matuka a kan man, ko da yake gwamnati mai ci na ikirarin fadada hanyoyin samun kudaden shigar.

A bara ne kasar ta farfado daga matsin tattalin arziki, wanda aka kwashe kimanin shekaru 25 ba ta shiga irinsa, a sanadiyyar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Danyen mai na Bonny Light wanda Najeriya ke samarwa na daga cikin mai mafi tsada a kasuwannin duniya.

Labarai masu alaka