Rushewar kofar Mata na haifar da dimuwa a Kano

Birnin Kano na da kofofi masu dogon tarihi.

Asalin hoton, Getty Images

A cikin watan Mayun da ya gabata, wata babbar mota ta auka kan ginin tarihi da ake kira Kofar Mata, lamarin da ya sa a yanzu sai kufenta.

A shekarun 1400 ne, Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, ya gina wannan kofa lokacin da ya fadada birnin Kano amma an sake gina kofar cikin 1985, kafin rushewarta a baya-bayan nan.

Al'umma dai a birnin Kano na ci gaba da bayyana jimami kan rushewar wannan kofa, mai dadadden tarihi.

Lokacin da BBC ta tuntubi wasu daga cikin mazauna birnin na Kano, sun ce ba su ji dadin faduwar kofar ba, musamman ganin tasirin da take da shi ga al'adun al'umma, kamar a lokacin hawan sallah, inda sarki kan fita da kuma dawowa ta kofar sa'ilin gudanar da hawan Nassarawa.

Sun kuma ce, rashin kofar na haifar da rudani ga baki wadanda ake wa kwatance da kofar a lokacin da za su shigo birnin na Kano domin harkokin kasuwanci da sauran sabgogi.

Masana sun ce kofar ta zamewa mutanen Kano garkuwa lokacin da Damagarawa suka kawo musu yaki a zamanin sarkin Kano Alu.