Hotunan yadda mota dauke da katako ta rufta kan motoci a Lagos

A ranar Talata da yamma ne wata babbar mota dauke da katako ta mirgino da katako mai tarin yawa daga kan gadar da take tafiya a kai, inda suka fada kan motocin da ke bi ta kasan gadar.

Wata babbar mota dauke da katako ce ta fado kan kananan motoci daga kan gada
Bayanan hoto,

Al'amarin ya faru ne a unguwar Ojuelegba da ke birnin Legas na kudu maso yammacin Najeriya.

Bayanan hoto,

Motoci da dama ne suka lalace sakamakon ruftowar katakon kansu. Ana fargabar cewar mutane da dama sun rasa rayukansu a hatsarin.

Bayanan hoto,

Wani karan mota ya tsira yayin da direban nasa ya mutu a hatsarin.

Bayanan hoto,

Kawo yanzu dai ma'aikatan agaji na kai wa wadanda lamarin ya rutsa da su dauki.

Bayanan hoto,

Ma'aikatan tsaftace birnin na ta kokarin share baraguzan katakon da ya zube a kan hanya.

Bayanan hoto,

Da ma kuma birnin Legas daya ne daga cikin biranen da aka fi samun cinkoson mutane da ababen hawa a Afirka.

Bayanan hoto,

Kawo yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba a hatsarin.