Jiragen yakin Isra'ila sun kai harin 'ramuwa' Gaza

An explosion in Gaza after Israeli air strikes on 20 June 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yakin sun kai harin ne kan sansanoni 25 da ke da alaka da Kungiyar Hamas

Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari sansanonin mayakan sa kai da ke Gaza bayan da Falasdinawa suka harba rokoki cikin yankin Isra'ila.

Wata sanarwa ta ce jiragen yakin sun kai harin ne kan sansanoni 25 da ke da alaka da Kungiyar Hamas domin mayar da martani kan lugudan wutar rokoki 45 da suka yi wa Isra'ilan.

An yi amannar cewa wasu jami'an tsaron Hamas biyu sun ji rauni kadan. Amma babu rahoton da ke nuna cewa an samu asarar rai ko jin ciwo daga bangaren Isra'ila.

Hare-haren dai na zuwa ne bayan da aka shafe makonni ana fito-na-fito a kan iyakar Zirin Gaza.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce dakarun Isra'ila sun kashe Falasdinawa fiye da 120 tare da raunata dubbai tun lokacin da aka fara zanga-zangar a watan Maris.

Dubban Falasdinawa sun fito zanga-zangar a kan iyaka don nuna goyon bayan ganin 'yan gudun hijirar Falasdinu sun samu 'yancin komawa matsugunansu na asali inda ya kasance Isra'ila a yau.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi dakarun Isra'ila da amfani da karfi fiye da kima.

Sai dai Isra'ila ta ce su na bude wuta ne kawai a kokarin kare kansu ko a kan mutanen da suke son su shiga yankinsu da karfin tuwo da sunan zanga-zanga.

Sojin Isra'ila ta ce ta kai hari da jiragen yaki sau uku cikin dare a wasu wuraren Hamas - ciki har da wasu sansanonin soji - bayan an harba rokoki a kan kauyuka da garuruwan Isra'ilan da ke kan iyakar Gaza.

Isra'ila ta kakkabo rokoki bakwai da mayaka suka harba, in ji rundunar sojin kasar.

An kuma aika jiragen leda dauke da wuta da mai zuwa cikin Isra'ila.

Hukumar yankin Eshkol Regional da ke kudancin Isra'ila ta ce rokoki biyu sun fadi kusa da wata cibiyar al'umma, kuma roka ta uku ta lalata gine-gine da motoci.

Kamfanin dillancin labaran Faladisnawa na Wafa, ya bayar da rahoton cewar a kalla mutum uku sun jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai kudancin Gaza - biyu sun mutu a Rafah, kuma daya ya mutu a Khan Younis.

Mazauna garin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar biyu daga cikinsu jami'an tsaron Hamas ne.

Wani mazaunin wurin ya shaida wa jairidar Haaretz ta Isra'ila cewar: "Kara da kuma fashe-fashen abubuwan sun tuna mana wani daren lokacin zafi na shekarar 2014," yayin da yake nuna ishara ga muhimmin fito-na-fito na baya-bayan nan da aka yi tsakanin Isra'ila da mayakan Falasdinawa a Gaza.

Rundunar sojin Isra'ila sun gargadi Hamas da cewar tana kokarin shigar da zirin Gaza da farar-hularta cikin wani tafarki mai tabarbarewa.

Ta kara da cewa: "Hamas ce ke da alhakin dukkan abin da ya faru a zirin Gaza kuma za ta samu sakamakon hakon farar-hular Isra'ila da gan-gan."

Kamfanin dillancin labaran AP ya bayar da rahoton cewar mai magana da yawun Hamas, Fawzi Barhoum, ya yaba wa hare-haren, amma bai ce kungiyar ce ta kai su ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani