Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin dan adam ta MDD

Sakataren harkokin wajan Amurka Mike Pompeo na kallon jakadar Amurka a MDD Nikki Haley lokacinda ta ke magana a ma'aikatar harkokin wajan kasar a Washington DC

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jakadar Amurka a MDD Nikki Haley da sakataren harkokin wajan Amurka Mike Pompeo suka sanar da matakin

Amurka ta janye daga hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, tana mai cewa "mattatara ce ta nuna son kai ta fuskar siyasa."

Jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta ce hukuma ce da ke cike da "munafinci", "wadda ta ke yi wa harkokin kare hakkin bil adama zagon kasa."

Hukumar da aka kafa a shekarar 2006, wadda ofishinta ya ke Geneva ta rika fuskantar suka a baya saboda ta amince da wasu mambobi masu alamar tambaya wajen kare hakkin bil'adam.

Sai dai masu fafituka sun ce matakin da Amurka ta dauka kan iya yin nakasu ga kokarin da ake yi wajen sa ido da kuma kawo karshen cin zarafin bil adama a duniya baki daya.

A lokacin da ta yi shelar ficewar Amurka daga hukumar, Ms Haley ta bayyana hukumar a matsayin "munafika wadda ta ke nuna son kai" wadda kuma ta ke "nuna wa Israila kiyaya."

Ta bayyana hakan ne tare da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, wanda ya yi Allah-wadai da hukumar, yana mai cewa tana kare kasashe masu "tauye hakkin bil'adama."

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Niki Harley ce Jakadiyar Amurka a MDD

Sukar da jami'an Amurkan suka yi ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da aka rika yi a kan matakin da Shugaba Trump ya dauka na jinjina wa shugaban kasar Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un, a taron da suka yi a baya-baya nan inda bai tabo batun cin zarafin bil adama ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

MDD ta sanya Koriya ta Arewa a cikin jerin kasashen duniya da ake cin zarafin bil adama kuma ta tattara bayanan cin zarafin bil dama a cikin kasar da ke gudanar da harkokinta cikin sirri.

Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da manufar gwamnatin Shugaba Trump ta kara zafafa, inda ake raba yara da iyayensu 'yan ci-rani a iyakar Mexico da Amurka.

Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya kira matakin a matsayin "kuskure."

Sakatare janar na MDD António Guterres ya mayar da martani kan matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga hukumar, yana mai cewa a ra'ayinsa yana son Amurka ta ci gaba da kasancewa mamba a cikin hukumar.

Mr Hussein ya kira ficewar Amurka a matsayin "abin takaicin, da ya zo da ba-zata". Sai dai Israila ta yi maraba da matakin.

Sharhin Nada Tawfik, wakiliyar BBC a New York

Wannan shi ne matakin kin amincewa da hadewar kasashen duniya a matsayin tsintsiya madaurinki daya da gwamnatin Trump ta dauka, kuma watakila hakan zai sa wasu kasashen duniya da suka dogara a kan Amurka wajen samun kariya da daukaka hakkin bil dama a duniya su nuna rashin jin dadinsu.

Tun farko babu jituwa a dangatakar da ke tsakanin Amurka da hukumar kare hakkin dan Adam.

Tsohuwar gwamnatin Shugaba Bush ta yanke shawarar kaurace wa hukumar a lokacin da aka kafa ta a shekarar 2006, saboda wasu dalilai irin wanda gwamntin Trump ta bayar.

A wancan lokacin John Bolton shi ne jakadan Amurka a MDD wanda a yanzu shi ne mai bai Shugaba Trump shawara kan tsaron kasa, kuma mai kakkausar sukar MDD ne.

A shekarar 2009 ne Amurka ta sake komawa cikin hukumar karkashin gwamnatin Barack Obama.

Akwai kawayen Amurka da dama da suka yi kokarin shawo kan Amurka a kan ta cigaba da kasancewa cikin hukumar.

Akwai kasashe da dama da suka amince da matsayin Amurka na sukar hukumar, wadanda suke ganin cewa ya kamata kasar ta ci gaba da taka rawa a cikin hukumar ta hanyar kawo sauye-sauye a maimakon ficewa daga ciki.

Bayyani kan hukumar kare hakkin bil adama

A shekarar 2006 ne MDD ta kafa hukumar domin ta maye gurbin ofishin kare hakkin dan adam wanda ya rika fuskantar suka a wurare da dama saboda ya amincewa kasashen da ba sa mutunta hakkin dan Adam shiga cikin kungiyar.

Kasashe 47 ne suka taru suka kafa hukumar, kuma sai bayan wa'adin shekara uku na shugaban hukumar ya zo karshe suke zabe domin samun wanda zai maye gurbinsa.

Hukumar ta UNHRC na taro sau uku a ko wacce shekara tare da yin nazari a kan ayyukan kare hakkin bil adama na mambobinta kuma ta bai wa ko wacce kasa damar yin bayani a kan abubuwan da suka yi domin inganta hakkin bil adama a kasashensu.

Hukumar kan tura kwararu masu zaman kansu zuwa kasashe domin su yi bincike, kuma tana kafa kwamitin bincike kan rahoton cin zarafin bil adam a kasashe irinsu Syria da Koriya Ta Arewa da Burundi da Myanmar da kuma Sudan Ta Kudu.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Hukumar na taro sau uku a ko wacce shekara kuma tana nazari kan mambobinta kan baututuwan kare hakkin bil adam

Shin me yasa Amurka ta fice?

Matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga cikin hukumar ya biyo bayan sukar da ta rika yi mata a shekarun da suka gabata.

Kasar ta ki shiga cikin hukumar da aka kafa a shekarar 2006, tana mai cewa babu banbanci tsakanin sabuwar hukumar da kuma tsohuwar, saboda sabuwar hukumar ta sake amincewa kasashe masu alamar tambaya kan hakkin dan adam shiga cikin hukumar.

A shekarar 2009 ne ta koma cikin hukumar karskashin Shugaba Barack Obama, kuma an sake zabarta a cikin hukumar a shekarar 2012.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun rika yin korafi a kan hukumar a shekarar 2013, bayan da aka zabi China da Rasha da Saudiyya da Algeriya da Vietnam a matsayin mambobin hukumar.