Hotunan yadda mata ke koyon tukin mota a Saudiyya

A daidai lokacin da Saudiyya ke shirin fara barin mata su yi tuki a ranar 24 ga watan yuni, kamfanin mai na kasar watau Aramco na koya wa ma'aikatanta mata tuki

Mai daukar hoton kamfanin dillancin labaran Reuters, Ahmed Jadallah da kuma 'yar jaridar kamfanin Rania El Gamal, sun kasance tare da mata ma'aikata 200 da ake koya wa tuki a sansanin koyon tuki da ke Dhahran mallakar kamfanin Saudi Aramco.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters

Daya daga cikin daliban ita ce Maria al-Faraj (wadda aka saka hotonta a kasa), wadda take daukar darasin tuki daga Ahlam al-Somali.

Student Maria al-Faraj with driving instructor Ahlam al-Somali Hakkin mallakar hoto Reuters

Baya ga koyon tuki, tana kuma koyon yadda za ta iya auna gejin mai da sauya taya da kuma muhimmancin amfani da madaurin kujerar mota.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters
A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters
A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters
A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters

Dage dokar da ta hana tukin matan wani muhimmin lokaci ne ga mata a Saudiyya. A baya a kan kama su ko a ci su tara idan an gansu suna tuki kuma sun dogara a kan maza 'yan uwansu wadanda za su tuka su idan za su fita ko yin hayar direba.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters

Amira Abdulgader wadda kwararriya ce wajen zanen gine-gine (ga hotonta a kasa) ta ce ranar 24 ga watan Yuni ta na shirin jan mahaifiyarta a mota.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters

"Zama a rike sitiyarin [na nufin ] ke kike jan ragaramar tafiyar," in ji Amira Abdulgader.

"Ni ce zan yanke shawarar lokacin da ya kamata a yi tafiya, abin da za a yi, da kuma lokacin da zan dawo.

"Muna bukatar mota domin mu yi ayyukanmu na yau da kullum. Mu na aiki, mu iyaye ne, muna sada zumunta ta kafafen sadarwa na zamani, muna bukatar fita - saboda haka muna bukatar sufiri. Zai sauya rayuwata."

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters

Kashi biyar cikin 100 na ma'aikatan kamfanin Aramco su 66,000 mata ne, kuma abin da haka ke nufi shi ne cewa watakila mata dubu uku za su shiga makarantar koyon tuki a cewar, Reuters.

A driving lesson at Saudi Aramco Driving Center in Dhahran Hakkin mallakar hoto Reuters

Duk da cewa an yaba wa Saudiyya game da soke dokar hana mata tuki, sai dai an samu ce-ce-ku-ce game da lamarin.

Masu fafituka da suka kasance suna neman a soke dokar sun samu sakonnin barazanar kisa, kuma an kama wasu daga cikinsu a watan Mayu kan cewar maciya amana ne kuma suna cewa suna aiki wa kasashen waje.

Hotuna daga Ahmed Jadallah.

Labarai masu alaka