Jami'ar OAU ta kori farfesan da ya nemi yin lalata da dalibarsa

Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su Hakkin mallakar hoto OAU
Image caption Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

Hukumomi a Jami'ar Obafemi Awolowo sun kori wani babban malami bayan samunsa da laifin neman yin lalata da wata daliba domin ba ta damar cin jarrabawa.

Mataimakin shugaban jami'ar Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya ce an kori Farfesa Richard Akindele ne bayan da ya amsa laifin kulla alaka da daya daga cikin dalibansa ta hanyar ba ta dace ba.

"Farfesa Akindele ya nemi yin lalata da Monica Osagie domin sauya maki kashi 33 da ta ci zuwa adadin da zai ba ta damar tsallakewa," a cewar Ogunbodede.

A watan Afrilu ne aka dakatar da Mr Akindele domin gudanar da bincike bayan da aka nadi muryarsa yana neman yin lalata da wata daliba domin ba ta sakamakon jarabawa.

Muryar ta Farfesa Akindele, wanda ke koyarwa a sashin harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi na jami'ar, ta bazu a shafukan sada zumunta.

Lamarin dai ya janwo ce-ce-ku-ce a kasar tare da nuna damuwa kan halayyar wadansu malamai game da dalibansu.

Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba bayan taron hukumar makarantar, Farfesa Eyitope Ogunbodede ya ce an tabbatar da muryar da aka rinka yada wa a watan Afrilu, kuma babban malamin bai musanta cewa tasa ba ce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

A lokacin da aka fara bincike kan lamarin, mai magana da yawun jami'ar ya shaida wa BBC cewa Monica ba ta halarci gayyatar da kwamitin ya yi mata ba, sannan ba ta tura da wakilci ko wani uzuri ba.

Babu tabbas ko daga baya ta halarci zaman kwamitin ko kuma ta aika wakili.

Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami'o'in Najeriya.

Labarai masu alaka