Kasafin kudi: Ban ji dadin cushen da majalisa ta yi ba – Buhari

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Bashir Ahmed/Twitter
Image caption Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin naira tiriliyon 9.1 ne a Abuja a ranar Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa game da wadansu sauye-sauye da majalisa ta yi a kasafin kudin bana, bayan ya sanya hannu kansa a ranar Laraba.

Shugaban ya sanya hannu a kan kasafin kudin na naira tiriliyon 9.1, bayan majalisar dokokin kasar ta amince da shi a tsakiyar watan Mayu.

Sai dai shugaban ya ce bai ji dadin yadda majalisar ta rage biliyoyin naira da aka ware don yin wadansu manyan ayyuka ba, a kasafin, wanda ya gabatar a watan Nuwambar bara.

Ayyukan sun hada da aikin tashar wutar lantarki ta Mambila da gada ta biyu ta kogin kwara da gina wadansu tituna da layin dogo da shirin gina gidaje na gwamnatin tarayya da wadansu ayyuka a bangaren kiwon lafiya da samar da tsaro da sauransu.

Sai 'yan majalisar sun ce sun yi sauye-sauyen ne domin tabbatar da adalci a tsakanin yankunan kasar kamar yadda tsarin mulki ya basu dama.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, ba tare da tuntubar bangaren zartarwa ba, majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14, wanda a ya sa a yanzu take da kasafin sama da naira biliyan 139 maimaikon naira biliyan 125 da aka ware mata tun da fari.

Shugaban kasar dai ya ce yana da aniyar gyara wasu muhimman sauye-sauyen da aka yi ta hanyar gabatar da wani kwarya-kwaryan kasafi ga majalisar ko kuma yin gyara ga wannan kasafin.

Martanin Majalisa

A nata bangaren, majalisar dai ta ce ta kara kasafin ne daga sama da naira tiriliyan 8 zuwa sama da tiriliyan 9 saboda hasashen cewa farashin danyen mai zai iya kai wa dalar Amurka 51 a kowacce ganga, ba dala 45 da shugaban ya sanya ba.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Abdulrazak Namdas ya ce dokar kasar ta ba su damar su yi ragi ko kuma kari a kasafin kudi a wuraren da suka kamata.

Game da ayyukan da aka ce 'yan majalisar sun kara, ya ce su ma wakilai ne "na jama'a kuma suna da damar sanya ayyukan da za su yi tasiri a rayuwar talaka," kamar yadda wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ta ce.

Hakazalika ya ce game da batun cewa majalisar ta kara wa kanta kudaden da yawansu ya haura naira biliyan 14 a kasafin kudin, ya ce kafin shekarar 2015 ana ware majalisar naira biliyan 150 a kasafin kudin.

"Amma sai aka rage zuwa naira biliyan 120 a shekarar 2015, aka kuma kara rage shi zuwa naira biliyan 155 a shekarar 2016, sai a shekarar 2017 da aka ware mana naira biliyan 125, bana kuma naira biliyan 139."

Ya ce: "ka ga ke nan har yanzu bai koma yadda aka saba yinsa ba kafin shekarar 2015, wato yadda ake ware mana naira biliyan 150," in ji shi.

Sharhi, Muhammad Kabir Muhammad, BBC Abuja

Alkaluma na baya-bayan nan da hukumar kididdiga ta Najeriya (wato National Bureau of Statistics ko NBS a takaice) ta fitar sun nuna cewa a watan Maris, kimar hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a Najeriya idan aka kwatanta da watan Fabrairu, daga kashi 14.33 cikin 100 zuwa kashi 13.34 cikin 100.

Wannan ne kuma wata na 14 a jere da kimar hauhawar ke raguwa.

"Wannan raguwar, a karo na 14 a jere tun daga watan Janairun 2017, ta nuna hauhawar ta ragu da kashi 0.99 cikin dari idan aka kwatanta da watan Fabrairun bana", in ji NBS.

Daga watan Fabrairun 2016 ne dai kimar hauhawar ta fara tashin gwauron zabi (lokacin da ta tashi daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu zuwa kashi 11.38 cikin dari) har ta kai matakin da aka yi shekara shida ba a kai makamancinsa ba a watan Janairun 2017, lokacin da ta kai kashi 18.72 cikin 100 (duba hoton da ke kasa).

Tattalin arzikin Najeriya a shekara uku da suka wuce

  • Mayu 2015: Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki
  • Fabrairu 2016: Farashin danyen man fetur ya fadi warwas zuwa kasa da $35 daga $115 a watan Yunin 2014
  • Fabrairu 2016: Kimar hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabi zuwa kashi 11.38 cikin dari daga kashi 9.62 cikin dari a watan Janairu
  • Afrilu 2016: A rubu'i na farko na 2016 kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta yi asarar sama da tiriliyan daya na Naira. Zuwa karshen shekarar kuma jimillar abin da ta yi asara ya tashi naira biliyan 604.
  • Yuni 2016: CBN ya karyar da darajar Naira
  • Agusta 2016: Tattalin Arzikin Najeriya ya durkushe a hukumance
  • Satumba 2017: Tattalin arzikin Najeriya ya farfado

Najeriya dai ita ce kasar da ta fi ko wacce arzikin danyen mai a Afirka kuma daya daga cikin manyan kasashen da suka fi arzikin man a duniya. Kuma tattalin arzikinta ya dogara ne matuka a kan man, ko da yake gwamnati mai ci na ikirarin fadada hanyoyin samun kudaden shigar.

A bara ne kasar ta farfado daga matsin tattalin arziki, wanda aka kwashe kimanin shekaru 25 ba ta shiga irinsa, a sanadiyyar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Danyen mai na Bonny Light wanda Najeriya ke samarwa na daga cikin mai mafi tsada a kasuwannin duniya.