Maganin rage radadi ya kashe mutum 456

Maganin rage radadi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani rahoto ya gano cewa fiye da marassa lafiya 450 sun mutu bayan an ba su maganin rage radadi wato painkillers masu karfi a wani asibiti da ke Birtaniya.

Wani kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar wannan lamari, ya ce idan aka yi la'akari da wasu bayanan da suka bata, to za a iya samun wasu marassa lafiyar 200 da suma irin wannan iftila'i ya shafa.

Wannan lamari dai ya faru ne a asibitin Gosport War Memorial Hospital,da ke Birtaniya.

Rahoton ya gano cewa, ba a damuwa da rayuwar marassa lafiya a kasar tun daga shekarar 1989 zuwa 2000.

Rahoton ya ce, Dr Jane Barton ce ta lura da yadda ake rubutawa marassa lafiya magani ba bisa ka'ida ba.

Ana dai rubuta magani ga marassa lafiya barka tai ba tare da la'akari da irin illar da shan sa zai haifar ba asibitin.

Firaministan kasar, Theresa May, ta bayyana wannan lamari da ya faru a asibitin a Gosport da cewa abin damuwa ne matuka gaya, sannan kuma ta nemi afuwa daga iyalan da lamarin ya shafa.

Babban sakatare a ma'aikatar kula da lafiya a kasar, Jeremy Hunt, ya shaida wa jami'an 'yan sanda da kuma masu shigar da kara na kasar cewa, zai yi nazari a kan rahoton, sannan ya duba matakin da za a dauka na gaba a kan wannan badakala.

Yawancin iyalan wadanda lamarin ya shafa, sun yi allawadai da asibitin, tare da neman da a shigar da asibitin kara a kotun hukunta manyan laifuka, saboda a cewarsu, wannan lamari na tare da sakaci a wajen aiki.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka