Me ya hana alkali halartar shari'ar Zakzaky a Kaduna?

Sheik Ibrahim Elzakzaky Hakkin mallakar hoto IMN
Image caption Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya dade yana saka kafar-wando daya daga gwamnati a Najeriya

An dage shari'ar da ake yi wa shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi ta 'yan Shi'a Sheik Ibrahim Zakzaky a birnin Kaduna saboda rashin halartar alkalin kotun.

Daya daga cikin lauyoyin da ke kare jagoran na 'yan Shi'a ya shaida wa BBC cewa an gaya musu cewa alkali bai halacci zaman kotun ba a don haka aka dage shari'ar.

Duka bangarorin biyu sun amince su sake bayyana a gaban kotu a ranar 11 ga watan Yuli.

A watan Afrilu ne gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi malamin tare da wasu mutum uku da laifuka takwas ciki har da kisan wani soja a shekarra 2015, lamarin da suka sha musantawa.

Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai lokacin da suka yi arrangama da 'yan shia a garin Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2015.

Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran 'yan Shi'a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.

Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan aka yi awangaba da wasu da dama.

Amma lauyan na 'yan Shi'a bai yi wani karin haske ba a kan dalilin da ya sa alkalin bai je kotun ba.

An rufe manyan hanyoyi a birnin na Kaduna da ke kusa da kotun gabanin shari'ar, in ji wakilin BBC a birnin, Nura Mohammed Ringim.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption 'Yan Shi'a na ci gaba da zanga-zangar neman a sako jagoransu

Rahotannin sun ce jami'an tsaro sun kuma hana 'yan jarida da suka hallara shiga cikin kotun.

An samu arangama tsakanin 'yan Shi'a da jami'an 'yan sanda lokacin da su ka yi zanga- zanga a kan hanyar Ahmadu Bello a ranar Laraba inda suka nemi a sako mu su jagoran nasu.

A farkon watan da ya gabata ne magoya bayan Sheikh Zakzaky suka fara zanga-zanga cikin lumana a kowace rana a birnin Abuja inda suka nemi a sako mu su jagoran nasu.

Sai dai sun sha ruwan hayaki mai sa hawaye daga jami'an tsaro wadanda suka zarge su da ta tada fitina, zargin da suka musanta.

Labarai masu alaka