An 'kashe jami'an tsaro 84' a Kamaru

Yang Philemon Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin kasar Kamaru ta ce 'yan awaren kasar sun kashe sojoji da 'yan sanda 84.

Firai ministan kasar, Yang Philemon, ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana wadansu laifuka da gwamnatin kasar take zargin 'yan awaren da aikatawa.

Mista Philémon ya kara da cewa masu fafitukar sun kashe wadansu jami'an gwamnati tare da yin garkuwa da su.

Kawo yanzu dai 'yan awaren ba su yi tsokaci ba game da zargin da gwamnatin ta yi musu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Har ila yau firai ministan ya ce masu fafitikar ballewar yankin renon Ingila na kasar suna amfani da shafukan sada zumunta wajen saka kyashi da tsoro cikin zukatan mutane tare da yin kira kan a bijire wa gwamnati.

An dade dai ana kai ruwa rana tsakanin gwamatin kasar da masu fafitukar neman 'yancin yankin renon Ingila wadanda suka ce ana nuna musu wariya.

Labarai masu alaka