Instagram ya ba da damar dora bidiyo mai tsawon sa'a daya

Kevin Systrom Hakkin mallakar hoto Instagram
Image caption Daya daga cikin mutanen da suka kirkiro Instagram Kevin Systrom

Shafin Instagram ya fitar da wani tsari da ya bai wa masu amfani da shafin damar wallafa bidiyo masu tsawo.

Tsarin na IGTV zai sa masu amfani da shafin su dinga dora bidiyo mai tsawo sosai sabanin da da ake iya dora bidiyon da bai wuce minti guda ba kawai.

Sai dai babu cikakken bayani a kan ko bidiyo mai tsawo zai ba masu amfani da shafin damar tallata hajjarsu, ko kuma biyan wadanda suka sa bidiyonsu kamar yadda ake yi a shafin YouTube.

A hirar da ya yi da BBC Newsbeat, mutumin da ya kirkiro Instagram Kevin Systrom, ya ce kamfanin ba ya cikin "hanzari wajen gano yadda haka zai yiwu."

IGTV zai rika nuna bidiyo kamar yadda mutane suke yi idan za su dauki hoto in ji Instagram.

Kevin ya ce: "Ya kamata a yi bidiyo mai kyau a waya."

Alex Brinnand kwarare ne kan harkar fasaha daga mujallar TenEighty Magazine, ya ce watakila tsarin IGTV ya sa shafin Instagram ya kasance mai tasiri sosai a shafukan sada zumunta.

Ya ce: "Kawo yanzu ba mu san irin karfin da Instagram ya ke da shi ba."

Na san akwai muhawara a kan abubuwan da ke faruwa a sauran shafukan sada zumunta da kuma yadda hakan zai kawo barazana, kuma wannan abu ne mai muhimanci."

An dai shirya liyafar cin abinci iri- iri a taron kaddammar da tsarin na IGTV a birnin San Francisco na Amurka.

Bidiyon mai tsawo na da muhimanci sosai ga uwar kamfanin Instagram wato Facebook.

Matasa da kuma masu shekaru fiye 20 su na yin kaura daga amfani da Facebook zuwa Instagram, saboda a ganinsu shafin facebook ya fi dacewa da iyayensu ko ma kakanninsu.

Don haka matasan sun fi amfani da shafin Snapchat da kuma YouTube .

Kamar yadda ya yi a baya, Instgaram zai yi amfani da tsarin IGTV, wajen kwaikwaiyon sauran takwarorinsa.

Yana ganin idan ya kashe makudan kudi kuma ya inganta kayansa to hakan zai sa kayansa su samu karbuwa ko da ya kasance cewa ya fitar da nasa a makare.

Tuni manhajar ta soma amfani da wani bidiyo irin na Snapchat inda masu amfani da shafin suke wallafa labarin da ya ke bacewa bayan kwana daya, ta hanyar sanya hoto ko bidiyo.

Kudi mai yawa

IGTV ba zai tallata hajja ba sai dai shugaban Instagram Kevin Systrom ya amince da cewa wannan kan iya sauyawa nan ba da jimawa ba.

Kuma zai iya zama kuskure idan ba su yi hakan ba.

A kan bukaci kudi mai yawa idan za a tallata kaya a bidiyo fiye da sauran tallace-tallacen da ake yi a shafin intanet.

Cibiyar bincike ta eMarketer ta yi hasashen cewa za a kashe dala biliyan 18 wajen tallata hajja ta hanyar amfani da bidiyo a shafin intanet a bana - abin da ke nuni da cewa an samu karuwa da kashi 22 cikin 100 kan na shekarar 2017.

Sabuwar manhajar za ta ba da damar samun karin kudi.

“Shafin Facebook ya gano cewa tallar da kan fito a shafin intanet ba tare da mai shafin ya latsa ba, ba ya tsairi sosai a bidiyo mara tsawo saboda mutane ba su cika mayar da hankali a kansu ba,” in ji Joseph Evans, daga kamfanin Enders.

"A kan haka idan kana son ka saka tallace-tallace a bidiyo to za ka bukaci bidiyo mai tsawo.”

Shafin Facebook na bayan YouTube a tsakanin bibiyar da matasa masu shekaru 18-24 suke amfani da shafukan sada zumunta, kuma sune rukunin shekarun da ma su tallace-tallace suke so, a cewar wani bincike da wata cibiya a Amurka ta yi.

Kuma muhimmin abu a nan shi ne masu amfani da shafin YouTube na shafe tsawon lokaci a cikin shafin, inda suke kallon tallace-tallace daban-daban.

Labarai masu alaka