Ranveer Singh da Deepika Padukone za su angwance

Ranveer Singh da Deepika Padukone Hakkin mallakar hoto India Today

Jarumi Ranveer Singh da jaruma Deepika Padukone, na daga cikin masoyan da ake so a masana'antar shirya fina-finai ta Indiya.

Ana dai ta yada jita-jita a kan cewa jaruman wadanda ke soyayya za suyi aure a karshen shekarar da muke ciki ta 2018.

To sai dai kuma a cewar wasu sabbin rahotanni da ake samu, jaruman za su yi aure ne a watan Nuwambar 2018.

A dan tsukun nan dai fitattun jaruman Indiya da dama sun yi aure, kamar Anushka Sharma wadda ta auri Virat Kohli, sai Sonam Kapoor da ta auri Anand Ahuja da kuma Neha Dupia wadda ta auri Angad Bedi.

Yanzu kuma hankali ya karkata kan Ranveer Singh da Deepika Padukone, wadanda suka jima suna soyayya a boye daga baya kuma suka sanar da cewa rade-radin da ake a kan soyayyarsu da gaske ne.

Rahotanni dai sun ce iyalan masoyan sun amince a yi auren ne a ranar 10 ga watan Nuwambar, 2018.

Hakkin mallakar hoto India Today

A baya dai Deepika Padukone ta yi soyayya ne da Ranbir Kapoor, daga bisani kuma suka bata, sai kuma tsutsun soyayyar ya koma kan Ranveer Singh, wanda sun fito a fina-finai da dama tare kamar Padmaavat da Goliyon ki Rasleela Ram Leela da Bajirao Matani da kuma Finding Fanny.

Tuni dai iyalan masoyan suka fara shirye-shiryen wannan kasaitaccen biki da aka jima ana jira wanda za a yi Mumbai.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka