An yanke wa malamin addinin musulunci hukuncin kisa a Indonesia

Aman Abdurrahman, da aka fi sani da Oman Rohman, a cikin kotun da ake yi masa sharia a Jakarta, da ke Indonesia, a ranar 22 ga watan yuni 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana kyautata zaton cewa malamin shi ne ya ke tafiyar da al'amuran magoya bayan kungiyar IS ta bayan fage a Indonesiya

An yanke wa malamin adinin musulunci a Indonesiya hukuncin kisa bayan da aka same shi da laifi wajen kitsa harin da 'yan ta'adda suka kai a shekarar 2016 a birnin Jakarta, inda mutum hudu suka hallaka.

An samu Aman Aburrahman da laifi wajen shirya harin da wani dan kurnar bakin wake ya kai a wurin shan shayi na Starbucks.

Malamin wanda ya yi wa kungiyar IS mubaya'a, shi ne jagoran wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci da ke kasar.

An danganta harin farko da aka kai a shekarar 2016 a Indonesiya a kan kungiyar IS.

Tun a shekarar 2010 ne Aburrahman, mai shekara 46, ya ke daure a gidan yari sai dai an fada wa kotun cewa ya rika kitsa hare-hare daga gidan kurkuku.

An samu jerin fashewar wasu abubuwa a Jakarta babban birnin kasar ciki har da gidan shan shayi na Starbukcs, da kuma wurin bincike na jami'an tsaro.

Fashewar ta faru ne a wani babban rukunin shaguna da kuma wani yanki na kasuwanci da ke kusa da ofisoshin jakadanci na kasashen duniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan bindiga sun kuma far wa gidan shan shayi na Starbucks, kuma sun yi musayar wuta lokacin da 'yan sanda suka iso.

Mahara biyu ne suka hallaka a ba-ta-kashin, yayin da biyu suka tayar da bam din jikinsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An shiga cikin rudani a birnin Jakarta lokacin da aka rika jin karar harbin bindiga da kuma fashewar wasu abubuwa

A hukuncin da alkalin ya yanke a ranar Juma'a ya ce an sami Abdurrahman da laifi wajen "aiwatar da ta'adanci".

Abdurrahman ya ce bai aikata laifi ba, kuma ya ce yana karfafa gwiwar magoya bayansa a kan su tafi zuwa Syria domin su yi fada tare da mayakan IS, sai dai bai ba da uamrnin kai hari a Indonesiya ba.

Shi ne jagoran kungiyar masu ta da kayar baya ta Jema'ah Ansharut Daulah wato (JAD), wadda a baya ta yi wa kugiyar IS mubaya'a, kuma ana ganin shi ne yake tafiyar da al'amuran magoya bayan kungiyar IS a Indonesiya ta bayan fage.

Indonesia, wadda ita ce kasar da ta fi yawan musulmi a duniya, ta rika fuskantar hare-hare daga wurin 'yan ta'adda a baya, amma wannan shi ne na farko da IS ta dauki alhaki.

A watan Yuni, an kai hare-haren kunar bakin wake kan wasu coci-coci da kuma ofishin 'yan sanda a Surabaya.

A kalla mutum 11 ne suka hallaka a hare-haren da aka kai wa mujami'un guda uku, wanda shi ne hari mafi muni tun bayan shekarar 2005 inda mutum 20 suka hallaka a harin bam na Bali.

Wasu iyali su shida ne suka kai hari a kan mujami'un ciki har da yara mata masu shekaru tara da 12.