Akon zai gina birni na musamman a Senegal

Akon Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shahararren mawakin nan watau Akon ya ce yana da anniyar fitar da kudin da ake musayarsu a intanet watau cryptocurrency da za a ba shi sunansa.

Da yake magana a bikin baje kolin bajinta na Cannes Lions Festival a ranar Litinin, mawakin ya ce ya yi amannar cewa kudin cryptocurrency kan iya "zama abinda zai farfado da Afrika."

'Akoin' ne sunan shirin na mawakin.

Shafin AKoin ya ce mawakin na son a saka manhajar a cikin kowace waya daga yanzu zuwa watan disemba.

Haka kuma Akon ya ce yana son ya gina wani gari da za a kira "crypto city" a Senegal yana mai cewa zai kasance "garin Wakanda na zahiri."

Hakkin mallakar hoto AKoin
Image caption Shafin mawakin AKoin ya yi karin haske kan sabon kudin

Kamar yadda aka tsara garin Wakanda a fim din Marvel Black Panther, Akoin ya yi alkawarin cewa garin zai kasance wuri mai ababen more rayuwa na zamani.

Shafin ya ce shugaban kasar Senegal ya ba Akoin "kyautar" fili mai fadin eka 2,000 inda zai gina garin wanda shi ma zai ba shi sunansa.

"Garin Akoin Crypto City zai kasance kusa da Dakar, babban birnin Senegal."

Ya kira shi garin mai ababen more rayuwa na zamani na farko da zai rika amfani da kudin Akoin wanda ake musayarsa a shafin intanet wanda za a rika amfani da shi wajan hada-hadar kudi.

A karkashin tsarin amfani da kudin Akoin mutane za su samu damar siyayya da kashe kudi ta hanyar amfani da wayoyinsu.

"Wannan zai sa iko ya koma hannun mutane kuma zai dawo da tsaro a cikin tsarin hada-hadar kudi ," in ji Akon.

"Zai ba mutane damar amfani da shi ta hanyoyi daban-daban domin inganta rayuwarsu ba tare da sun jira gwamnati ta yi mu su ababen more rayuwa ba."

Sai dai Akon ya amince da cewa ba shi da masaniya kan kayayyakin da zai bukata domin cimma wannan burin.

Shin me ake nufi da kudin cryptocurrency?

Cryptocurrency kudi ne da ake musayarsa a shafin intanet ba tare da babban bankin ya sa ido akansa ba.

Yana amfani da sakon sirri domin tabbatar da tsaro da kuma sahihancin hada-hadar da aka yi.

Zai yi wuya a sake yin wani irinsa ko jabunsa.

Na farko kuma wanda ake ganin shi ne ya fi samun karbuwa shi ne Bitcoin, wanda wani mutum wanda ba a san ko shi wane ne ba ya kirkiro amma yana amfani da suna Satoshi Nakamoto a shekarar 2009.

An samu wasu shahararrun 'yan wasan kwaikwaiyo da mawaka da suka zuba jari a cikin harkar, ciki har da Katy Perry, da 50 Cent da Ashton Kutcher.

Sauran ayukkan Akon a Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akon tare da Ms. Kine Gueye Thiam wadda suka kafa kungiyar Konfidence tare a 2007

AKoin na cikin ayukkan da Akon ya tabbatar da yana gudanarwa a Afrika.

A garin Missouri aka haifi Akon kuma asalinsa dan Senegal ne, kuma a can ne ya yi akasarin kuriciyarsa.

A shekarar 2007 ce ya kafa kungiyar agaji ta Konfidence tare da hadin gwiwar wata mata, wadda ta ke taimakawa yara marasa galihu kan ilimi da kiwon lafiya a yammacin Afrika da Amurka.

Ya kuma kafa kungiyar samar da makamashi ta Akon Lighting Africa project a shekarar 2014, wanda shafin Akon ya ce ta samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana a kasashen Afriika 18 ya zuwa yanzu .

Labarai masu alaka