An yi jana'izar Sarkin Fadar Kano, Sule Gaya

Sarkin Fada Hakkin mallakar hoto Sarkin Fada's Family
Image caption Marigayi Alhaji Sule Gaya ya rasu yana da shekara 92 a duniya

An yi jana'izar Sarkin Fadar Kano Alhaji Sule Gaya ranar Juma'a da safe a birnin Kano.

Sarkin Fada ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke unguwar Durumin Iya cikin birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

An yi jana'izar tasa ne a fadar Kano da ke kofar Kudu da misalin karfe 9 na safiyar Juma'a, kuma Sarki Muhammadu Sunusi na II ne ya ja sallar.

Alhaji Sule Gaya, wanda yana daga cikin ministocin jamhuriya ta farko a Najeriya, ya rasu yana da shekara 92 a duniya.

Ya mutu ya bar mata biyu da 'ya'ya da kuma jikoki masu yawa.

Daga cikin 'ya'yansa akwai Yusuf Sule Gaya tsohon shugaban kwalejin fasaha da kuma Hauwa Sule Gaya, tsohuwar kwamishiniyar mata ta jihar Kano, kuma babbar ma'aikaciyar gwamnatin tarayya kafin ta yi ritaya a baya-bayan nan.

Sauran manyan 'ya'ansa sun hada da Saude Sule Gaya da Ahmed Sule Gaya da Yusuf Sule Gaya da Sa'adatu Sule Gaya da Amina Sule Gaya da Nasiru Sule Gaya da Abubakar Sule Gaya.

Hakkin mallakar hoto Sarkin Fada's Family
Image caption Sarkin Fada da daya daga cikin 'ya'yan jikokinsa
Hakkin mallakar hoto Sarkin Fada's Family
Image caption A lokacin bikin karamar sallar nan da ta gabata Gwamna Abdullahi Ganduje ya kai masa ziyara

Labarai masu alaka