Turawa na sake karbe gonaki a Zimbabwe

Fararen fata da yawa ne aka kwace wa gonaki lokacin mulkin Mugabe Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manoma fararen fata da dama ne tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya kora daga gonakinsu a kasar.

To amma yanzu akwai alamun cewa gwamnatin da ke ci za ta bar su su koma domin ci gaba da noma filayen na su.

Shekara guda da ta gabata ne aka tursasa wa wani manomi mai suna Rob Smart da iyalansa barin filayen nomansu.

Kuma ba shi kadai ba ne, domin akwai da yawa irin wadanda haka ta faru da su a zamanin Robert Mugabe.

Yanzu dai sabuwar gwamnatin kasar ta taimaka wa Rob, ya sake karbar filinsa na noma.

Sai dai wasu daga cikin fafaren fatar na da tababa kan sahihancin alkawarin da gwamnati ta yi na cewa za ta mayar musu da gonakin nasu, kasancewar wasu ka'idojin da ke cikin yarjejeniyar sun nuna cewa gwamnati za ta iya kwace filin da ta bayar haya cikin kwana 90.

Wasu bakaken fata sun yi maraba da shirin mayar wa fararen fatar gonakin na su.

Rob, ya ce yanzu sun samu tsaro sosai fiye da kowanne lokaci, domin gwamnati da sojoji sun tabbatar masu cewa za su iya kiran su a duk lokacin da suke bukata.

Sai dai manomin ya ce, yanzu akwai jan aiki a gabansu, na ganin sun mayar da gonakin na su kamar yadda suke a da, bayan da aka lalata tare da sace wasu daga cikin kayan aiki.

Labarai masu alaka