An kai mummunan hari a gangamin Firaministan Habasha

Habasha Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutane ne suka halarci gangamin na nuna goyon baya ga Mista Abiy

Hukumomi a Habasha sun ce mutum guda ya mutu yayin da gwammai suka samu mummunan rauni bayan harin da aka kai a wani babban gangamin da Firaminista Abiy Ahmed ke jagoranta.

Tun da farko Mista Abiy ya ce mutane da dama ne suka mutu.

Kafar watsa labaran telebijin ta kasar ta ce kimanin mutane miliyan hudu suka halarci gangamin.

A cikin jawabinsa ya yi kiran hadin kan kasa da sasantawa.

Kuma Firamnistan na cikin jawabi aka kai harin, lamarin da ya hargitsa dubban mutanen da suka halarci gangamin.

Firamnistan ya bayyana lamarin a matsayin "yunkurin da bai yi nasara ba ga wadanda ba su son hadin kan Habasha."

An yi nasarar ficewa da Abiy daga wajen taron da dubban mutane suka halarta a dandalin Meskel da ke birnin Addis Ababa a ranar Asabar.

A shafinsa na twitter, Ministan lafiya na kasar ya ce mutum guda ne ya mutu, yayin da 154 suka jikkata, kuma 10 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Mista Abiy ya zama Firaminista ne bayan Hailemariam Desalegn ya yi murabus a watan Fabrairu.

Shi ne shugaba na farko daga 'yan kabilar Oromo, wadanda suka shafe shekaru uku suna zanga-zangar adawa da gwamnati wacce ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Tun hawan Abiy kan mulki, ya fara aiwatar da sabbin sauye-sauye, da suka hada da toshe kafofin watsa labarai na telebijin da shafukan intanet.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai harin ne bayan Mr Abiy ya kammala jawabi

Sannan ya ce a shirye yake ya tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Eritrea da aka sanya wa hannu a 2000 bayan kawo karshen yaki na shekaru biyu.

Kasashe da dama da suka kunshi Amurka da Japan da Eritrea sun yi Allah wadai da harin da aka kai wa gangamin na Firaminista Abiy.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Jami'an tsaro a inda aka kai harin

Labarai masu alaka