'Yan hamayya ke son halaka ni - Mnangagwa

Shugaba Mnangagwa a lokacin gangamin yakin neman zabe a Zimbabwe Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Mnangagwa a tsakiya a lokacin gangamin yakin neman zabe a Zimbabwe

Zimbabwe ta nuna kaduwarta matuka bayan shugabanta Emmerson Mnangagwa ya tsalake rijiya da baya a lokacin fashewar wani abu da ya ce kokari ne na hallaka shi.

Mista Mnangagwa ya bayyana cewa akwai abokan hamayya a cikin Jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar wanda watakil su ke da hannu a harin da aka kai lokacin da ya ke kokarin barin wajen gangamin yakin neman zabe a Bulawayo.

Akalla mutum 10 ciki har da wasu ministocinsa biyu aka jikkata.

Shugaban ya bayyana harin da wani yunkuri na matsarota, da ba zai iya haifar da tsaiko ga zaben da ake shirin gudanarwa a watan gobe ba.

Akwai kwarin-guiwar cewa Mista Mnangagwa zai lashe zaben, sai dai masu sharhi na cewa yana da makiya da ke jin haushi kawar da mulkin Robert Mugabe da ya yi.

Labarai masu alaka