Iraq ta 'kashe shugabannin IS 45' a gabashin Syria

map

Iraki ta ce ta kashe wasu mayakan kungiyar IS su 45 a wani hari da jiragen sama a gabashin Syria, kuma a cikinsu akwai manyan shugabannin kungiyar.

An kai hari ne kan wasu gidaje uku da aka ce shugabannin IS din na gudanar da wani taro a garin Hajin.

Yankin Euphrates na cikin yankuna na karshe da ke karkashin ikon IS a Syria.

Wadanda ka kashen sun hada da wani babban kwamanda IS, da jami'in watsa labaranta da manzon shugaba Abu Bakr al-Baghdadi na musamman.

A watan Disambar bara, gamayyar kasashe karkashin jagorancin Amurka suka ce sun kwato kimanin kashi 98 cikin 100 na yankunan da a da ke hannun kungiyar ta IS.

Labarai masu alaka