Turkiyya: Erdogan ya lashe zaben shugaban kasa

Erdogan supporters celebrate outside the AK party headquarters in Istanbul, Turkey Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya bayan Shugaba Erdogan sun fita bisa titunan Istanbul da suka sami labarin nasararsa a zaben

Shugaban hukumar zaben Turkiyya ta bayyana Recep Tayyip Erdogan a matsayin wanda ya lashe zaben shugana kasar a zagayen farko.

Sadi Guven ya ce shugaban ya sami gagarumin rinjaye a cikin kuri'un da aka kada, amam bai bada wani karin bayani ba.

Kafofin watsa labaran kasar na fitar da rahotanni masu cewa Mista Erdogan ya sami kashi 53 cikin 100, kuma an kammala kirga kimanin kashi 99 cikin 100 na dukkan kuri'un da aka kada.

Shi kuma babban mai adawa da shi, Muharrem Ince ya sami kashi 31 cikin 100 na kuri'un.

Masu adawa da shugaba Erdogan ba su mika wuya ba a hukumance, amma sun ce za su cigaba da fafutukar ganin demokradiyya ta sami gindin zama a kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hotunan 'yan takarar zaben shugaban kasar Turkiyya

Tun da farko, 'yan adawan sun nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben da aka rika bayyanawa a kafofin watsa labaran kasar.

A ranar Juma'a za a bayyana cikakken sakamakon zaben.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Shugaba Erdogan tare da matarsa Emine na karban gaisuwa daga magoya bayansu a gaban ofishin jam'iyyarsa a Ankara
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Muharrem Ince bai gamsu da yadda aka rika gbayyana sakamakon zaben ba

Akwai wasu 'yan takara su hudu da suka tsaya a wannan zaben, amma babu wanda ya sami fiye da kashi takwas da rabi na kuri'un.

Mista Ince ya ce zai kwana a ofishin hukumar zaben da ke birnin Ankara domin ya tabbatar da an yi adalci, kamar yadda ya bayyana a wani sako na Twitter.

Ya kuma nemi magoya bayansa da kada su bari a yi magudin zabe.

Labarai masu alaka