Canada ta tura karin sojoji Mali

Ana yawa fuskantar hare-hare a yankunan kauyukan Mali
Image caption Ana yawa fuskantar hare-hare a yankunan kauyukan Mali

Wata karamar tawagar dakarun Canada sun isa Mali domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

Tawagar, da ake sa ran ta bada taimakon abubuwan da ake bukata, za ta rufawa sauran dakaru da ke yankin baya a cikin makonni masu zuwa.

Canada ta amince dakarunta su yi wannan aiki na wanzar da zaman lafiya har zuwa watan Yulin 2019.

Adadin dakarun Majalisar Dinkin Duniya dubu 15 yanzu haka ke aiki a Mali tun shekara ta 2015.

Cikin wannan adadi an kashe soji sama da 100 duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnati da bangaren 'yan tawaye suka sanyawa hannu shekaru 3 baya.

Labarai masu alaka