Dan mawaki D'banj ya nutse a ruwa

D'banj
Image caption Yaron mai shekara daya ya nutse ne a cikin ruwan da ake ninkaya

Rohotanni sun ce dan shahararen mawakin nan D'Banj da matarsa ‚Äč‚ÄčLineo Didi Kilgrow mai shekara daya ya mutu, bayan ya nutse a cikin ruwan ninkaya na gidansu da ke birnin Lagos.

Duk da cewa D'Banj bai ba da tabbacin mutuwar Daniel Oyebanjo III kai tsaye ba, amma ya saka bakin hoto a shafinsa na Instagram yana mai cewa: "Wannan lokacin ne na jarabta, kuma na yi imani da hukunci ubangiji."

D'Banj dai ya kasance a Birnin Los Angeles na Amurka don halartar bikin karrama mawaka na BET na bana a lokacin da dansa ya rasu, a cewar kafofin watsa labarai na gida.

Rahotanni sun ce an kai gawar yaron mutuware.

Mutane da dama sun nuna alhinin game da rashin da mawakin ya yi.

Mawaki Davido, wanda ya halarci bikin na BET, ya nuna alhininsa ga D'banj a jawabin da ya yi lokacin da ya karbi kyautar mawakin da ya nuna bajinta sosai a duniya.

Sanata Ben Murray Bruce, ya bi sahun sauran 'yan Najeriya masu yi wa D'banj ta'aziyya.

Ya ce a Twitter: "Na yi matukar bakin ciki game da mutuwar danka. Mutuwar yaro abin takaici ga k wanne mahaifi. A madadin iyalina da ni, muna son mu nuna alhininmu dangane da wannan rashin."

Labarai masu alaka