An kama mutumin da ya 'kashe' maguna dubu a Kenya

Mage Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani dan kasar Kenya ya amsa laifin kashe maguna fiye da 1,000, inda ya rika sayar da namansu ga jama'a kamar yadda kafafen yada labarai suka bayyana.

Wadansu 'yan unguwar da mutumin yake zaune ne suka gan shi yana fede wata mage a garin Nakuru a yammacin birnin Nairobi a shekarar 2012.

Ya amsa laifin cewa ya kashe magunan ne bayan da wadansu matasa suka kusan kashe shi da duka, a cewar jaridar Kenya's Star ruwaito.

Daga nan, sai 'yan sanda suka kama mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba. Hakazalika kuma ba a bayyana laifukan da za a tuhume shi a kan su ba, kodayake a ranar Litinin ne ake saran gurfanar da shi.

An haramta kashe maguna da sayar da namansu a kasar Kenya, kamar yadda wani ji likitan dabbobi mai suna Githui Kaba ya bayyana wa kafar yada labarai ta Nairobi News.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka