Indiya ce kasar da mata suka fi shiga hatsarin cin zarafi

Wasu tsoffin al'adu na tasiri ga 'yan cin mata a wasu kasashen Asiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu tsoffin al'adu na tasiri ga 'yan cin mata a wasu kasashen Asiya

Wani bincike da gidauniyar Thomas Reuters ta fitar, ta bayyana India a matsayin kasar da ta fi hatsari ga mata.

Rahotan binciken ya ce mata sun fi fuskantar barazanar cin zarafi ta hanyar lalata da kyara ko tsangwama daga wasu dadaddun al'adu, da kuma safarar su da kuma musgunawa.

Afghanistan ita ce ta biyu da Syria ta uku a jerin jadawalin kasashen.

Cikin kasashen yammaci d'aya tilo da aka ambato a wannan rahoton ita ce Amurka, wadda ke a matsayin ta 10 a rahoton.

A cewar gidauniyar, mata a Amurka na fuskantar tursasawa da fyade, kuma ba sa samun daman kwato hakkinsu.

Gidauniyar Thomas, ta ce ta tattara bayananta ne a tattunawar da ta yi da kwararu akan harkokin mata su 550 tsakanin watan Maris zuwa Mayu.