Atiku Abubakar ya tallafa wa wadanda bala'in Bauchi ya shafa

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku/Twitter

Bayanan hoto,

Atiku Abubakar ya gana da wasu sarakunan gargajiya a jihar

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga mutanen da bala'in guguwa da ruwan sama ya shafa a jihar Bauchi.

Da yake magana a fadar Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwan Adamu, Atiku Abubukar wanda ke neman jam'iyyar adawa ta PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasa, ya yi addu'ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu a bala'in, ya kuma mayar wa da wadanda suka rasa dukiya arzikinsu.

Ziyarar ta sa ta zo ne kwanaki kadan bayan wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar, inda shi ma ya jajanta wa wadanda lamarin ya shafa.

Ruwan sama da iska da aka yi a makon da ya gabata ne suka lalata gidaje da makarantu, sannan iskar ta haifar da asarar rayuka a wasu sassan jihar.

An shafe sa'a guda ana iskar wacce ta jawo duhu a garuruwa da dama na jihar.

Bayan wannan iftila'i ne kuma wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Azare na karamar hukumar Katagum, inda ta shafe tsawon daren har zuwa wayewar gari tana ci.

Gobarar ta jawo asarar dumbin dukiya da kawo yanzu ba a tantance adadinta ba.

Atiku Abubakar ya ce "na zo da naira miliyan 10 domin taimaka wa wadanda lamarin ya shafa, kuma ina fatan Allah ya kawar da sake afkuwar irin wannan bala'i a nan gaba".

Asalin hoton, Atiku/Twitter

Bayanan hoto,

Atiku Abubakar ya kuma yi addu'a ga jama'ar da wannan ibtila'i ya shafa

A jawabinsa, mai martaba sarkin Bauchi, ya ce gudummawar da tsohon shugaban kasar ya bayar ta nuna irin soyayyar da yake yi wa mutanen Bauchi.

"Muna matukar nuna godiya ga kaunar da kake nuna wa jama'ar Bauchi".

Sannan ya yi alkawarin cewa kudin da aka bayar za su isa ga mutanen da aka bayar domin su.

Daga nan kuma tawagar Alhaji Atiku Abubakar ta wuce zuwa garin Azare domin jajanta wa mutanen da bala'in gobarar ya shafa, wacce ta rusa shaguna fiye da 1,000 a babbar kasuwar garin.