Kashe-kashe: Buhari ya kai ziyara Filato don yin jaje

Daya daga cikin wadanda rikicin Filato ya rutsa da su
Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun ce sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a hare-haren

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jos, babban birnin jihar Filato, saboda kisan da aka yi wa fiye da "mutum 200" a rikicin makiyaya da manoma.

Mai taimakawa shugaban kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad, ya ce shugaban zai yi wa jama'ar jihar jaje sannan ya gana da shugabannin al'umma da masu ruwa da tsaki domin "samar da dawwamammen zaman lafiya" a kasar.

Har ila yau shugaban ya yi kira da a kwantar da hankali kuma jama'a su ci gaba da zama da juna cikin lumana.

Wani shugaban al'umma a jihar ya shaida wa BBC cewa akalla mutum 200 aka kashe lokacin da wasu "Fulani makiyaya" suka kai harin ramuwar gayya a wasu kauyuka 11 na Riyom, Barikin Ladi da kuma Jos ta Kudu.

Sai dai wani jami'i a kunigyar Fulani ta Miyetti Allah ya yi Allah-wadai da harin, sannan ya yi kira da a hukunta duk wadanda ke da hannu a lamarin.

Hukumomi 'yan sanda sun ce akalla mutum 86 ne suka mutu a hare-haren, wadanda aka kai a karshen makon da ya gabata.

Sai dai bai yi karin bayani kan ko shugaban zai ziyarci wuraren da rikicin ya faru ba ko kuma zai tsaya ne kawai a Jos.

Ko a ranar Litinin ma Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya shafe sa'o'i yana tattauna wa da shugabannin al'umma a jihar domin shawo kan matsalar.

Sannan ya nemi hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA da ta tallafa wa wadanda da lamarin ya shafa.

Yadda lamarin ya faru

Wasu rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar Alhamis bayan da 'yan kabilar Berom suka farma wasu Fulani makiyaya, inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Daga nan ne kuma aka ce wani hari na ramuwar gayya da Fulani suka kai ya kai ga kisan wasu karin mutanen da dama.

Yankin ya dade ya na fama da rikici tsakanin kabilun da ke rigima kan mallakar filaye.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin, sannan ya sha alwashin hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Tare hanya

Rahotanni dai na cewa mutanen yankin da ake rikicin suna tare hanya su na kashe mutanen da 'ba su ji ba, ba su gani ba,' wadanda yawancinsu matafiya ne da ke fitowa daga jihohin arewa maso gabas kamar su Bauchi da Gombe da Yobe, zuwa Abuja.

Su waye Fulani Makiyaya?

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Wani makiyayi yana bai wa dabbobinsa ruwa

  • Suna daga cikin ƙungiyar makiyaya mafi girma a duniya kuma ana samun su a yammaci da kuma yankin tsakiyar Afrika, daga Senegal zuwa jamhuriyar Tsakiyar Afrika
  • A Najeriya wasu sun cigaba da zama a matsayinsu na makiyaya, yayin da wasu suka koma birane
  • Fulani makiyaya suna yin akasarin rayuwarsu a daji ne, ba kamar mutanen da ke zama a cikin birane ba, kuma suna da alaƙa da waɗannan rikice-rikicen
  • Suna kiwon dabbobinsu a yankuna da dama, inda suke yawan yin rikici da al'ummomin da galibin aikinsu noma ne
  • Ana yawan dangantasu da ƙabilar Hausa, saboda tsawon lokacin da suka shafe suna zama tare
  • Fulani sun taka muhimmiyar rawa a ƙarni na 19 wajen farfaɗo da addinin Musulunci a Najeriya.

Me ke kawo rikicin?

Ana tunanin ce-ce-ku-ce a kan abubuwan more rayuwa kamar su gonaki da yankunan da ke da burtali da ruwa ne ke jawo rikici tsakanin makiyaya da kuma manoma.

Fulani makiyaya kan iya tafiya mai nisa tare da dabbobinsu domin nema musu abinci. Mafi yawan lokuta, suna daukar makamai domin kare dabbobin nasu.

Asalin hoton, other

Bayanan hoto,

Rikicin ya rutsa da matafiya da dama kamar wadannan da ba a tantance ko su wa ye ba

Suna yawan rikici da manoma wadanda ke yawan cewa suna lalata musu amfanin gona kuma ba sa kula da inda dabbobin nasu ke zuwa.

Fulanin na zargin cewa manoma waɗanda ke ƙoƙarin satar shanunsu - suna cewa suna ƙoƙarin kare kansu ne.

A da, rikicin a yankin tsakiyar Najeriya aka fi yi, inda kiristoci ƙabilar Birom da ke jihar Plateau suke kisan ramuwar gayya ga Musulmai da makiyaya.

Yadda sauyin yanayi ya ke shafar burtali ya sa Fulani makiyaya sun kara matsawa zuwa kudancin Najeriya domin neman ruwa da ciyawa.

Wannan ya ƙara faɗaɗa rikicin ta inda ake cigaba da fuskantar munanan tashe-tashen hankula a kudancin ƙasar, ana ƙara jin tsoron cewar rikicin zai yi barazana ga haɗin kan da dama ya ke tangal-tangal tsakanin ƙabilun Najeriya.