Kotu ta daure mutumin ya yi samosa da naman mage

Mutumi ya amsa aikata laifi
Bayanan hoto,

An yanke masa hukuncin daurin shekara 3

An yanke wa mutumin da saura kiris a kona shi a Kenya bayan da aka kama shi yana fige mage hukuncin daurin shekara uku a gidan kaso bayan da kotu ta same shi da laifin sayar da nama.

James Kimani ya amsa aikata laifin kashe mage tare da sayar da namanta ga mutane da basu san cewa naman mage bane.

Jaridar The Daily Nation ta kasar Kenyan ta halarci zaman kotun da ke garin Nakuru domin jin hukuncin da za a ynake masa.

Tun farko BBC ta bayar da labari a kan yadda ya shafe shekara biyar yana sayar da samosa da ya yi da naman mage ga mutane.

Dokar kasar ta hana cin naman mage a matsayin abinci.

Sai dai ya yinda ba a amince da cin naman mage a Kenya ba, akwai wasu kasashe da ke cin naman magen.

Ana kuma cin naman mage a kasashen China, da Vietnam da kuma Koriya.

A baya-baya nan ne mutumin ya amsa laifin kashe maguna 1,000 inda ya rika sayar da namansu ga jama'a.