Mahaifiya ta kashe danta kan wayar salula a Najeriya

Yaron da mahaifiyarsa ta cinnawa wuta Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Jama'a sun rika wallafa hoton yaron da mahaifiyarsa a kafofin sada zumunta

Wata mahaifiya ta kona danta, abin da kuma ya yi sanadin mutuwarsa .

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a yankin Amuzukwu da ke birnin Umuahia na jihar Abia a Kudancin Najeriya.

Kakakin 'yan sanda na jihar, Geoffrey Ogbonna wanda ya tabbartawa BBC da lamarin, ya ce mahaifiyar mai 'yaya uku mai suna Chinyere tana tsare a hannun jami'an 'yan sanda.

Ya ce suna tuhumarta da cinnawa danta mai shekara 12 wuta kan batan katin adana bayanai na waya wato (memory card).

"Bayanan da na tattara sun ce lamarin ya faru ne sakamakon katin adana bayanai na wayar wata mata da ya bata, sai ta daure hannun yaronta, ta zuba masa kananzir sannan ta cinna masa wuta".

An wuce da yaron mai suna Odum Prince asibitin gwamnati da ke garin Umuahia bayan aukuwar lamarin amma ya rasu da safiyar ranar Talata.

Kakakin asibitin Darlington Mmadubuko ya shaida wa BBC cewa marigayin ya "kone sosai kuma an yi masa kulawar gaggawa a lokacin da ya iso asibiti".

'Yan sanda sun ce kawo yanzu suna gudanar da bincike kan lamarin, kuma sun tabbatar cewa gawar yaron na ajiye a mutuwaren asibitin gwamnatin tarayya da ke Umuahia.

Kafofin sada zumunta a Najeriya sun rika wallafa hotunan yaron da mahaifiyar ta sa.

Ba kasafai irin wadannan al'amura masu daure kai ke faruwa a Najeriya ba, kuma ko suna faruwa ba su fiye fito bainar jama'a ba.

Labarai masu alaka