Buhari ya kai ziyara jihar Katsina don yin jaje

Shugaba Buhari da Sarkin Katsina Hakkin mallakar hoto NIGERIAN PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Katsina don jajanta wa mutanen da bala`in iska da ambaliyar ruwa ta shafa.

Dubban mutane ne iftila`in ya shafa a kananan hukumomin Katsina da Charanchi da kum Musawa, a cikin `yan makwannin da suka wuce, lamarin da ya hadda asarar rayuka da dukiya mai yawa.

A makon jiya ne shugaban kasar ya kai irin wannan ziyarar a jihar Bauchi don jajanta wa wadanda masifar iska da gobara ta auka musu.

Shugaban ya shiga birnin Katsina ne a wani yanayi na juyayi, don haka babu wani tanadi da aka yi don sauraron ribibin da kuma dandadazon jama`a ko dogin jawabai da irin na siyasa da aka saba gani.

Shugaban ya gana da kadan daga cikin wadanda bala`in ya shafa ne a matsayin wakilai, a fadar mai martaba sarkin Katsina.

Daga nan ya jajantawa wadanda abin ya shafa, inda ya ce yana tausaya musu, kuma yana bayyana iftila`I daban-daban da ke shafar al`ummar Najeriya a dan tsakanin da cewa "kaddara ce da ta wuce sanin dan Adam, amma duk da haka gwamnati za ta agaza musu."

Gwamnatin jihar dai ta ce masifar iska da ambaliyar ta auku ne har sau biyu a cikin wani gajeren lokaci, amma irin asarar da ta haddasa, baya ga asarar rayukan jama`a, ta lalata dukiyar da ta kai fiye da naira biliyan biyu.

Sabanin wasu masifun da suka auku a baya, wadanda shugaban kasar bai samu zuwa jaje da kansa ba, a dan tsakanin nan Shugaba Buhari ya matsa-kaimi wajen yin tattaki don jajanta wa al`umma a bangarorin kasar.

Abin da ya faru a jihar Katsina ya dan kwana-biyu da faruwa, kasancewar ya riga na jihar Bauchi.

Sai dai duk da haka shugaban sai ya zabi ya fara zuwa Bauchi.

Wasu dai na danganta wannan sabuwar himma ta shugaban da kare murmurewar da yake yi daga jinyar da ya yi fama da ita.

Sai dai wasu kuma na zargin cewa ziyarar shugaban da nasaba da siyasa ganin cewa saura `yan watanni a yi babban zaben kasar.

Amma mai taimaka wa shugaban kan harkar yada labarai, Mista Femi Adisina ya musanta hakan.

"Ko kadan ba haka ba ne, saboda Shugaba Buhari mutum ne mai tausayi. Duk lokacin da wani abu ya faru da ke bukatar kulawarsa, to yakan saurara. Ba ya cusa siyasa a duk abin da ya shafi rayuwar bani Adamu".

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN PRESIDENCY

Labarai masu alaka