Kotun koli ta amince da dokar Trump ta hana wasu Musulmi shiga Amurka

Protesters at the US Supreme Court.

Asalin hoton, Reuters

Kotun Kolin Amurka ta goyi bayan matakin da gwamnatin Donald Trump ta dauka na hana mutane daga wasu kasashen Musulmi shiga kasar.

Lower courts had deemed the ban unconstitutional, but the US top court has reversed this decision in a 5-4 ruling announced on Tuesday.

Kananan kotuna sun yi yanke hukuncin cewa hanin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, amma kotun kolin Amurka ta sauya batun a wani hukunci da aka yanke da rinjayen 5-4 a ranar Talata.

Dokar ta hana mafi hawan mutane shiga Amurka daga kasashen Iran, Libya, Somaliya, Siriya da Yemen.

Ana kallon hukuncin da kotun ta yanke a matsayin nasara ga gwamnatin Trump.

Amma kungiyoyin 'yan gudun hijira da masu rajin kare hakkin dan-adam sun yi tir da dokar.

Babban Alkali John Roberts ya bayyana cewa dokar tana "cikin ikon shugabancin".

"Gwamnatin ta bayyana hujja ta tsaron kasa a kan dalilin da ya sa ta yi dokar domin tsallake tunanin da ake yi a kai. Ba mu bayyana ra'ayi game da yadda aka tsara dokar ba."

Jim kadan bayan Kotun Kolin, Shugaba Donald Trump ya watsa labarin a shafinsa na Twitter.

Omar Jadwat, daraktan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amurka (ACLU) da kuma baki, ya ce hukuncin yana daya daga cikin "babbar gazawa" ta Kotun ta nuna a tarihi.